Kasar Gambiya na fuskantar kiki-kaka | Siyasa | DW | 22.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kasar Gambiya na fuskantar kiki-kaka

Kasar Gambiya na fama da dambarwar siyasa bayan da Shugaba Yahya Jammeh ya ce ba zai sauka ba ya na nan daram a kan mulki har sai kotu ta yanke hukunci a watan Janairu.

Dangane da wannan hali dai da ake ciki a Gambiya, kafar yada labaran gwamnatin na baiyana abin da gwamnatin ke so jama'a su sani ne kawai. A saboda haka ne wasu kafofin yada labaru masu zaman kansu ke kokarin tacewa da samar da sahihan bayanai ga jama'a.

Tashar DW ta sami hira da babban editan kafar yada labarai ta Foroyaa Sam Sarr daya daga cikin kafofin yada labarai masu zaman kansu a kasar ta Gambiya. Ya kuma baiyana halin da kasar ke ciki a yanzu.

"Ina gani akwai 'yar damuwa, ana dari-dari, amma baki daya abin da jama'a ke cewa shi ne lokaci yay i a gare shi ya sauka. Sakamakon da hukumar zabe ta bayar daidai ne, a saboda haka ya kamata ya karbi kaddara kamar yadda zamani ya zo da shi. Wannan shi ne ra'ayin da jama'a ke baiyanawa. Haka nan kuma wasu na kallonsa a matsayin babbar matsala da ka iya tada zaune tsaye a kasa, alhali an san Gambiya a matsayin kasa mai zaman lafiya da kwanciyar hankali."

 

Gambia Präsidentschaftswahl Adama Barrow (Getty Images/AFP/M. Longari)

Adama Baro dai murna na neman komawa ciki

Shugaban kasar Jammeh wanda ya shafe shekaru 22 a karagar mulki ya yi burus da yunkurin shiga tsakani da Kungiyar ECOWAS ta yi domin jan hankalinsa ya sauka ya mika mulki cikin kwanciyar hankali da lumana.

Wannan matsayi da shugaba Yahya Jammeh ya dauka dai ya sanya fargaba da zaman zulumi a zukatan 'yan kasar ta Gambiya. To shin ko bangaren zabbaben shugaba Adama Baro sun maida martani ga sanarwar ta Jammeh.  Sam Sarr Editan kafar yada labarai ta Foroyaa ya yi bayani da cewa:

Gambia Präsident Yahya Jammeh & Nigerias Präsident Muhammadu Buhari (Reuters)

Zuwan su Shugaba Buhari na Najeriya bai sauya komai ba a Gambiya kawowa yanzu

" Kawowa yanzu ban sami bayani daga masu aiko mana da rahotanni ba, amma ina jin bisa ga halayyar da bangaren sabon shugaban ya nuna a shirye su ke domin yin masalaha cikin ruwan sanyi, amma idan shugaban kasar ya fito da irin wadannan zafafan kalamai, a na su bangaren sun shirya karbar mulki su na jiran cikar wa'adin shugaban ne kawai wanda shi ne 19 ga watan Janairu. A wannan rana za'a rantsar da sabon shugaba, kuma zai kasance lamari haramtacce ga shugaban kasar ya cigaba da kasancewa a karagar mulki, ba na jin za su shiga yin wani cacar baki da shugaban kasar saboda suna so komai ya tafi lami lafiya, kuma ba su yi kiran wata zanga zanga ba".

ECOWAS ta amince za ta bukaci Jammeh ya sauka amma kuma sun ce za su cigaba da kokarin shiga tsakani kuma tawagar masu shiga tsakanin za ta kasance ne karkashin jagorancin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da tallafin shugaban Ghana John Mahama, tun daga wannan lokaci dai babu wani bayani sabo sai dai jita jita da jama'a ke yadawa.

Sauti da bidiyo akan labarin