Kasar Australiya na shirye-shiryen samun sabon Firaminista bayan shekaru takwas | Labarai | DW | 14.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Australiya na shirye-shiryen samun sabon Firaminista bayan shekaru takwas

Malcolm Turnbull wanda yake hamshakin mai arziki kuma tsohon ma`aikacin banki ya sami rinjayen kuriu 44 daga cikin 54

Kasar Australiya na shirin samun sabon Firaminista shekaru takwas bayan da jam'iyyar da ke jan ragamar gwamnatin kasar ta zabi Malcolm Turnbull biyo bayan rade-radin da aka dade ana yi daga bangaren masu kada ku'ria.

Turnbull wanda yake hamshakin mai arziki kuma tsohon ma'aikacin banki ya sami rinjayen kuri'u 44 daga cikin 54 kamar dai yadda mai tsawatarwa a majalisar jam'iyyar Scott Buchholz yake fada wa manema labarai jim kadan bayan taronsu a birnin Canberra na kasar. 

Haka kuma an zabi ministan harkokin wajen kasar Julie Bishop a matsayin mataimakin jam'iyyar wacce ta kulla kawance da jam'iyyar National Party da ta samu gagarumin rinjaye a zaben shekara ta 2013.