Kasar Afirka da ta fara bin tsarin dimokradiyya | Amsoshin takardunku | DW | 10.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Kasar Afirka da ta fara bin tsarin dimokradiyya

Kasar Ethiopia ce ta farko da ta fara bin tsarin dimokradiyya a nahiyar Afirka, dubi da irin tsarin shugabanci da take dashi na tsawon shekaru masu yawa.

Ko da shi ke a can baya, manufar "Dimokradiyya" ita ce gwamnatin jama'a, wadda jama'a ne suka zaba kuma take mulki domin tabbatar da maslahar jama'a, amma a yanzu ta rungumi wata sabuwar fassara, musamman a baya bayannan.

A yanzu "Dimokradiyya" na nufin kyakkyawan shugabanci, wanda a karkashinsa, zababbiyar gwamnati, ko kuma hukuma za ta tabbatar da cewar, ta samar da ingantaccen tsarin Ilimi, da Kiwon lafiya, da kuma bunkasa tattalin arzikin al'umma, ta yadda jama'a za su sami aikin yi domin rungumar dawainiyar rayuwarsu ta yau da kullum.

Hakanan a karkashin wannan tsarin, gwamnati za ta kare 'yancin jama'a da hakkokinsu, wanda ya hada da 'yancin fadin albarkacin baki da kuma zaben shugabanni, game da mutunta zaben da suka yi, ba tare da muzgunawa ba.

Za ku iya sauraren shirin a kasa!

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin