Kasancewa cikin fargaba saboda Ebola | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 22.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Kasancewa cikin fargaba saboda Ebola

Hukumomin kasar China sun hana wasu matasan Najeriya na tawagar 'yan wasan Olympics shiga gasar matasa a Nanjing saboda fargabar kwayoyin Ebola.

To har wayau dai cutar Ebola na ci gaba da daukar hankalin jaridun na Jamus. A labarin da ta buga mai taken kasancewa cikin fargaba jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tsokaci ta yi ga abin da ya faru da tawagar matasa 'yan wasa daga Najeriya lokacin da suka isa kasar China don halartar wasannin Olympics na matasa a yankin Nanjing da ke gabashin China makon da ya gabata.

Ta ce da saukarsu filin jirgin sama hukumomin China sun tsare kana sun kebe wasu 'yan wasa daga kasashen Afirka ta Yamma suka yi ta sa musu ido bisa fargabar cewa watakila suna dauke da kwayoyin cutar Ebola da ke yaduwa a wasu kasashen Afirka. Hakazalika bayan ya shawarta da hukumar lafiya ta duniya Kwamitin kasa da kasa na Olympics ya hana wasu 'yan dambe biyu da mai ninkaya daya daga Najeriya da kuma Guinea shiga gasar saboda kasadar harba kwayoyin Ebola, sannan an ci gaba da auna zafin jikinsu. Saboda haka ba abin mamaki ba ne da 'yan wasan suka fusata cewa an nuna musu wariya kuma suka sanar da janyewa daga wasa bayan da farko sun ki halartar bikin buden wasan. Jaridar ta ce wannan ya zama abin takaici ga wadanda abin ya shafa amma a wurin da suka koman fargabar ta fi yawa.

Ebola cuta mai nasaba da al'adu

Ebola Isolierstation Charite Berlin 11.08.2014

Tsadar magani ta hana a gudanar da cikakken bincike kan Ebola

Ita kuwa jaridar Berliner Zeitung ra'ayoyin wasu masu karanta jaridar ta buga game da cutar ta Ebola. Inda wani a cikinsu ya ce Ebola cuta ce mai hatsarin gaske wadda kuma ke da nasaba da wasu al'adu. To amma da mai zai fraru inda cutar a jihar Florida ta Amirka ta bulla amma ba a Afirka ba. Ai da tuni an dakile ta, domin Ebola ba sabuwar cuta ba ce da yanzu haka ta addabi daruruwan mutane a Afirka. Masana kwayoyin cuta sun santa tun 1976 farkon bullarta a tsohuwar kasar Zayya wato Kongo yanzu. Amma badakalar a nan shi ne tun kimanin shekaru 40 aka san irin hatsarinta kuma ko da yake akwai maganinta amma ba a gudanar gwaje-gwaje isassu a kai ba bare a amince da allurarta bisa dalilin cewa tana da tsada."

Mata da ci gaban nahiyar Afirka

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung a wannan makon tsokaci ta yi game da rawar da mata za su iya takawa wajen kyautata zamantakewa da samun ci gaba a Afirka.

Afrika Textilindustrie

Mata da ci gaban tattalin arzikin Afirka

Ta ce yanzu haka hukumar kungiyar tarayyar Afirka da hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya sun fara wani shirin kyautata matsayin mata a fannin tattalin arzikin Afirka. Kawo yanzu mata a Afirka na fuskantar kalubale wajen samun bashi daga banki don kafa kamfanoni sannan suna da karancin ilimi idan aka kwatanta da maza. Amma idan hukumomi suka tallafa musu za a samu sauyi mai ma'ana, kamar yadda ake gani a kasar Ruwanda, inda tallafin gwamnati ga mata ke da karfi kuma kwalliya ke mayar da kudin sabulu. Shi ma Bankin Duniya ya yi imanin cewa matakin ilimantar da mata matasa da Ruwandar ke aiwatarwa a fannonin sana'o'in hannu da noma da tallata hajojinsu na zama dalilin da ya sa kasa ke samun bunkasar tattalin arziki na tsawon shekaru.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu