Zabtarewar kasa ta kashe rayuka a Kamaru
October 30, 2019Talla
Akalla mutane guda 42 suka rasa rayukansu bayan da aka samu zabtarewar kasa a Bafoussam da ke a yammacin Kamaru, gidaje da dama lakar da ta malala ta binne a sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a yankin. A cikin wani jawabin ta kafofin sadarwa na gwamnati, shugaba kasar Paul Biya ya yi ta'aziya zuwa ga iyalen wadanda suka yi rashin. A cikin watan Yuli na shekara bara ma an samu zabtarewar kasar a Limbe da ke a yankin Ingilishi na Kamaru inda mutane biyar suka mutu.