Kasa ta halaka rayuka a Kwango | Labarai | DW | 17.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasa ta halaka rayuka a Kwango

Wani sabon ibtila'in zaftarewar kasa ya yi sanadin mutuwar mutane 40 a lardin Ituri da ke a jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango, kamar yadda mahukuntan kasar suka tabbatar.

Wani ibtila'in zaftarewar kasa ya halaka akalla mutane 40 a lardin Ituri da ke a jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango. Wani mataimakin gwamnan lardin ya ce lamarin ya auku ne bayan ruwan sama mai karfi da aka tabka a wani kauyen da galibi masunta ke zaune a cikinsa.

Lamarin na faruwa ne yayin da a Freetown babban birnin kasar Saliyo kuwa, aka shiga rana ta biyu ta zaman makoki tare da binne daruruwan mutanen da ambaliya ta halaka a ranar Litinin da ta gabata.

Akwai wasu sama da mutum 600 da suka bace har kuma ya zuwa yanzu babu labarinsu a bala'in na Saliyo. Tuni dai gwamnatin kasar ta yi yekuwar agajin kasashen duniya, don kai mata dauki a halin da ta tsinci kanta ciki.