Kasa ta binne sama da 300 a Guatemala | Labarai | DW | 04.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasa ta binne sama da 300 a Guatemala

Ba wannan ne karon farko da ake samun zaizayar kasa a wannan kasa ba, sai dai a wannan karon mutane kalilan ne kadai aka gano kawo yanzu.

Iyalan wadanda suka hallaka a zaizayar kasar da ta afku a kasar Gautemala, sun gudanar da addu'o'i cikin juyayi, suna rike da fitilar kandir, dan tunawa da mutane 87 da aka tabbatar sun hallaka, a yayin da ake cigaba da nemo wasu 300 da kasa ta rufe, wadanda su ma ake fargabar wata kila sun riga mu gidan gaskiya.

Masu aikin ceton dai na cigaba da kokarin gano wadanda suka rayu. Iyalan da suke rayuwa a wannan yanki na kudu maso gabashin Guatemalan, inda wannan hatsarin ya afku sun ce ba wannan ne karon farko da bala'i irin wannan ke afka musu ba, a 'yan shekarun da suka gabata ma, an taba yin irin wannan zaizayar kasar inda nan ma suka rasa wasu daga cikin 'yan uwansu.

Wani mutumi, direban tasi mai suna Alejandro Lopez mai shekaru 45 na haihuwa, wanda ya zanta da kamfanin dillancin labaran Reuters, ya ce ya gano gawawwakin 'ya'yansa mata biyu da jikarsa guda amma har yanzu bai cire ran cewa zai gano matarsa a raye ba.