1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar zaman zullumi a arewacin Najeriya sakamakon harin bama-bamai

Mohammad Nasiru AwalMay 22, 2014

Yayin da manyan kasashen duniya suka fara ba da gudunmawa don yaki da tarzoma a Najeriya, yankin arewacin kasar na fama da hare-haren bam.

https://p.dw.com/p/1C4Zc
Anschlag in Jos, Nigeria
Hoto: picture alliance / AP Photo

Mutane da yawa dai ne suka rasu sannan wasu da dama suka jikkata a hare-haren bam da suka addabi wasu biranen arewacin Najeriya irin su Kano da Jos. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan kungiyar Boko Haram ke ci gaba da kashe mutane tare da kona wuraren zamansu a arewa maso gabacin Najeriyar.