Karuwar ′yan gudun hijirar Sudan ta Kudu a Yuganda | Labarai | DW | 26.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karuwar 'yan gudun hijirar Sudan ta Kudu a Yuganda

Tuni dai shirin zaman lafiya da aka cimma a shekarar 2015 tsakanin masu gaba da juna a kasar ta Sudan ta Kudu ya shiga rudani abin da ya kara yawan masu kaura.

Ban Ki-moon Besuch in Juba Südsudan

'Yan gudun hijirar Sudan ta Kudu a lokacin ziyarar Majalisar Dinkin Duniya

Fiye da mutane 37,000 sun yi kaura daga Sudan ta Kudu zuwa makobciyar kasar Yuganda cikin makonni uku da suka gabata, bayan yaki tsakanin masu gaba da juna da ya yi sanadi na rayukan daruruwan mutane kamar yadda hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a ranar Talatan nan.

Tuni dai shirin zaman lafiya da aka cimma a shekarar 2015 tsakanin masu gaba da juna a kasar ta Sudan ta Kudu ya shiga rudani bayan ci gaban gwabzawa tsakanin dakarun da ke mara baya ga Shugaba Salva Kiir da jagoran adawa Riek Machar da shugaban ya maye gurbinsa Taban Deng Gai a matsayin sabon mataimaki, lamarin da ke kara nuna takun saka da bangarorin suka koma bayan Machar ya fice daga Juba.

A cewar ofishin na Majalisar Dinkin Duniya mutanen da suka yi kaura zuwa Yuganda a cikin makonni uku sun ninka wadanda suka je kasar cikin watanni shida na farkon wannan shekara ta 2016 inda cikin wannan lokaci aka samu sama da mutane 33,000 da suka shiga kasar ta Yuganda dan neman mafaka.