1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar rasa rayukka a tekun Mediterranean

July 14, 2021

A wani sabon rahoto da hukumar kula da kaura ta Majalisar Dinkin Duniya IOM  ta fitar, na nuni da cewa adadin wadanda suka rasa rayukkansu a tekun Bahar Maliya, yayin da suke kokarin tsallakawa zuwa Turai ya rubanya.

https://p.dw.com/p/3wRfi
Libyen I Flüchtlinge im Mittelmeer
Hoto: Sergi Camara/AP/dpa/picture alliance

Rahotan ya ce akalla mutane 1,146 suka salwanta daga watan Janairu zuwa Yunin wannan shekarar da muke ciki ta 2021 a tekun na Mediterranean, wadanda galibinsu suka hada da mata da yara kanana.

Da ma dai kungiyoyin bayar da agajin gaggawa da dama sun sha yin gargadin cewa, karanci kayan aikin ceto ka iya jefa masu keta tekun ta barauniyar hanya cikin hatsari a daidai lokacin da gwamnatocin kasashen Turai suka dogara kan kasashen arewacin Afirka.