Karuwar masu shan taba a Zimbabwe | Zamantakewa | DW | 10.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Karuwar masu shan taba a Zimbabwe

Gwamnatin kasar na kokarin hada kai da kungiyar Lafiya ta Duniya wato WHO domin binchiko dabar da za'abi don takaita karuwar yara kanana da ke shan taba.

Wani binchiken da DW ta gudanar, ya gano cewa munin lamrin ya zarta ga shan taba sigari kawai, amma yara kananan yanzu a kasar ta Zimbabwe, sun tsunduma wajen shaye-shayen wuy-wuy da sauran ababen sa maye.

Binciken baya-bayanan da kungiyar WHO ta gudanar, ya gano cewa kashi 20 cikin dari na matasan Zimbabwe 'yan shekaru 13 izuwa 17, duk suna zugar taba. Lovemore Mumbengeranwa da ke jagorantar ma'aiktar lafiyan kasar ya yi karin haske bisa abinda binciken ya nunar.

"Wannan ya bayyana mana cewa matasanmu a makarantun Zimbabwe na matukar zukar taba. Hakan na nufin dole kasar mu ta dau matakan takaita bazuwar taba. Don rage kudin da ake batar kan cututtukan da suka shafi shan taba"

Sayar wa yara 'yan kasa da shekaru 18 taba dai haramun ne a Zimbabe, amma binciken na WHO ya nuna cewa, wannan dokar a rubuce ne kawai take. Matsalar tattalin arziki a Zimbabwe na daga abinda ke sa masu shaguna ke sayar wa yara sigari. Kamar yadda wannan matashi dan shekaru 16 ke bayyanawa.

"Akwai kwayoyi ma da mutum zai iya sha. Irin wadannan kwayoyin an yi su ne ga masu tabin hankali. Idan kasha suna kara kuzari. Ana samunsu a asibitin mahaukata, kuma can muke sayosu. An yi su ne don masu jinya, amma mu ma mukan sayosu"

Mosambik Goldwäsche Flash-GalerieShi kuwa wannan matashin ga dalilin da ya bayar.

"Wannan duk rashin aiki ne ke haddasa shi, idan muna da aikin yi da ba za mu zunduma shan taba da ababen sa maye ba. Idan muna da aikin da ake biyanmu albashi, ai babu wanda zai damu da shan ababen sa maye"

Shungu Munyati, ita ce ta jagoranci binciken da WHO suka dauki nauyin gudanarwa a Zimbabwe, ga kuma karin haske da ta yi.

"Shan taba ga matasa duk ya rataya ne ga salon zamananci na shaye-shaye da sauransu, hakan kuwa zai tsunduma mutum ga lamarin da ya jibanci cututtukan da ake kamuwa ta hanyar jima'a kamarsu HIV da sauransu. Kaga abun dai duk na dangantaka da juna ne."

Gwamnatin kasar Zimbabwe dai ta kadu da sakamakon binciken da aka samu na yawan masu shan taba. Domin kuwa shan taba musamman ga masu kananan shekaru, yakan haddasa cutar kansar huhu da sauransu. Don haka masanan ke cewa ana bukatar sa dabarun kwadaitar wa matasa gujewa shan taba, a cikin jadawalin makarantun kasar ta Zimbabwe.