1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban kaura tsakanin jama'a

Zainab Mohammed Abubakar
December 1, 2021

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana samun karuwar yawan kaurar jama'a tsakanin kasa da kasa a bara, duk da matakan rufe kan iyakokin kasashe saboda annobar COVID 19.

https://p.dw.com/p/43hQi
Seenotrettung im Mittelmeer
Hoto: Hermine Poschmann/Mission Lifeline/dpa/picture alliance

A sabon rahotonta, hukumar kula da kaura na majalisar ta nunar da cewar an samu karuwar yawan mutanen da suka kauracewa kasashensu na asali da wajen miliyan 281 a shekarar da ta gabata.

Hakan na nuni da kari daga mutane miliyan 272 da aka samu a 2019, kazalika karin sama da miliyan 200 a kan na shekara ta 1970, lokacin da aka sanar da kaurar mutane wajen miliyan 84 tsakanin kasashe matalauta da masu karfin tattalin arziki.

Sai dai duk da haka hukumar ta MDD ta jaddada cewar, ba don corona ba da yawan masu gudun hijirar da ya fi haka.