Karuwar jama′a da kalubalen samar musu ababen more rayuwa | Siyasa | DW | 11.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Karuwar jama'a da kalubalen samar musu ababen more rayuwa

Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 11.06. na kowace shekara don nazarin karuwar jama'a da nufin kyautata jin dadinsu.

Bukin wannan shekarar, ya mayar da hankali ne akan kiwon lafiyar jama'a da yadda karuwar jama'a ba zai hana masu samun rayuwa mai inganci ba.

Kididdigar yawan jama'ar duniya ta shekara ta 2011 ta nuna cewa yawan jama'ar ya wuce miliyan dubu 7 kuma hakan ya saka alamar tambaya akan kalubalen samar musu da abababen more rayuwa da suka hada da ilmi da kuma kiwon lafiya hadi da ci-gaba mai dorewa.

Ba shakka taken wannan shekarar na bukuwan ranar ta yawan jama'a a duniya na bukatar wayar da kan jama'a akan hanyoyin inganta kiwon lafiyar su, karanci kayan kiwon lafiya, zai ci gaba da yin tarnaki ga ci-gaban al'umma in dai ba hukumomi sun cike gibin da ake samu ba sakamakon karin haifuwa da ake yi.

Malam Abubakar Mai Akwai, shi ne babban darektan hukumar kidayar Jama'a ta kasa a Sokoto, ya ce yawan jama'a wani kalubale ne ga hukumomi wajen inganta samar musu da kiwon lafiya, don haka da sake.

Das Maitama Hospital – ein typisches staatliches Krankhaus in Nigerias Hauptstadt Abuja Bilder stammen von DW-Redakteur Jan-Philipp Scholz und sind in Abuja, Nigeria aufgenommen im September 2011.

Asibitin Maitama, Abuja, Najeriya

Kokarin gwamnati na samar da asibitoci

Su kuma hukumomi a nasu bangare na cewa, suna sane da yadda jama'a ke karuwa a yankunansu kuma har ma sun dukufa wajen ganin an samar da ababen kiwon lafiyarsu da kuma inganta rayuwar iyalai musamman a karkara, kamar yadda Comrade Ibrahim Jibril, mai baiwa gwamnan Sokoto shawara akan samar da kiwon lafiya a karkara ke tabbatar wa.

Tuni dai hukumomi ke fitowa da shirye-shirye na inganta lafiyar al'umma amma ba kasafai ake samun inganci da kuma dorewar su ba, shi yasa Malam Chika Wakili ke ganin kamata yayi hukumomi su sauke nauyin da ke kansu na samar da kiwon lafiya ga jama'arsu.

Modupe Adebayo ist Chefin des Asejere Markts in Makoko. Foto: DW/Katrin Gänsler aus Lagos

Kula da lafiyar matan karkara

Matan karkara su ne suka fi shan wuya in ana maganar samar da kiwon lafiya, kuma yawan haifuwa na da matukar yawa a yankunan, wanda a cewar Malama Hadiza Bello, ya kamata hukumomi su fi mayar da hankali wajen inganta kiwon lafiyar jama'a a karkara saboda rashin wayewa da kuma karancin ilmi da ke addabrsu.

Al'ummomi ma, na da tasu rawa da za su taka wajen ganin yawan karuwar jama'a bai hana kowa samun cikakkar kulawa ta kiwon lafiya ba, don ko ba komai, barin 'ya'ya mata zuwa karatun kiwon lafiya zai taimaka wajen rage kyamar zuwa asibitoci da har yanzu wasu iyalai ke yi a wannna yankin na Najeriya.

Mawallafi : Aminu Abdullahi Abubakar
Edita : Saleh Umar Saleh

Sauti da bidiyo akan labarin