Karuwar hare-hare a wajen jana′iza a Libya | Labarai | DW | 08.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karuwar hare-hare a wajen jana'iza a Libya

Wani dan harin kunar bakin wake ya tada bam daidai lokacin da ake gudanar da jana'izar wani babban jami'in 'yansanda a wata makabarta da ke Benghazin kasar Libya.

Wani dan harin kunar bakin wake ya tada bam daidai lokacin da ake gudanar da jana'izar wani babban jami'in 'yansanda a wata makabarta da ke Benghazin kasar Libya.

A kalla mutane biyu ne aka bada labarin sun jikkata baya ga dan kunar bakin wake da ya rasu a makabartar ta al-Hawari daidai lokacin da ake yi wa Kanar Kamal Bezazah sutura bayan da ya rasu sakamakon raunukan da ya samu a wani harin bam da ya rusta da shi.

Rahotanni daga kasar ta Libya dai na nuna yadda yanzu mahara kan tada bam a wuraren da ake yin jana'iza ko zaman makoki a dan tsakanin nan, lamarin da al'ummar kasar suka ce ya na ci musu tuwo a kwarya.

Kanar Bezazah dai na daga cikin jami'an tsaron Libya da suka yi shuhura wajen sukar irin farmakin da ake kaiwa jami'an tsaro wanda sau tari kan yi sanadiyyar rasuwarsu.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu