1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar cin hanci da rashawa a hukumomin Najeriya

July 9, 2013

Kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta Transparency International ta fitar wani rahoto da ya nuna cewa ba’a samu wani sauyi ba game da yakar matsalar a Najeriya.

https://p.dw.com/p/194iF
LAGOS, NIGERIA - JULY 15: A detail of some Nigerian Naira,(NGN) being counted in an exchange office on July 15, 2008 in Lagos, Nigeria. (Photo by Dan Kitwood/Getty Images)
Hoto: Getty Images

Batun cin hanci da rashawa da rub-da ciki a kan dukiyar talakan Najeriya da ake zargin masu rike da madafan iko da ma 'yan korensu na yi ba sabon abu bane a Najeriya, kama daga sama da dalla biliyan 16 da aka kashe a fannin samar da wutar lantarki da har yanzu bata samu ba, baya ga makudan kudaden da aka karkatar dasu da sunan samar da tallafin Mai, duk dai tatsuniyar gizo ce da bata wuce ta koki.

To sai dai sakamakon  binciken da kungiyar ta Transparency International ta gudanar a game da matsalar cin hanci da rashawa ya kara tabbatar da zargin da aka dade ana yi ne. Abin da Dakta Hussaini Abdu, shugaban kungiyar Action Aid mai yaki da talauci da cin hanci ya ce abin takaici ne, duk da cewa babu kage a wannan rahoton, amma  kuma akwai dalilan.

Ya ce "Wannan ba mamaki domin yanzu kusan shekaru uku ko hudu kenan gwamnati bata damu da batun cin hanci da rashawa ba, kusan yanzu ma musu suke yi in ka ce masu cin hanci na nema ya yi katutu sai su ce maka alambaran. Shi kansa shugaban kasa da aka ce ya fito ya yi bayani a game da batun kudin da ya mallaka ai ki ya yi, sai dai ya yi a asirci, saboda haka babu wani tasiri ga batun yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, matsalar na karuwa ne a kusan kullum."

Nigeria police detain suspicious people April 28, 2011 near a polling station during a security operation to stave ballot box-snatching in Bauchi, the capital of Bauchi state, nothern Nigeria. Two Nigerian states hit hard by deadly riots after presidential elections went back to the polls for governor races Thursday amid a security lockdown and with scores still displaced. Soldiers accompanied electoral officials to polls in Kaduna and Bauchi states and the electoral commission scrambled to find some 2,000 workers to replace those who refused to show up because of fears of violence. Police and military personnel in armoured vehicles patrolled the streets of Kaduna city, the capital of the same state, and set up roadblocks to search cars. Police kept a close eye on Bauchi city, the capital of that state. AFP PHOTO / Tony KARUMBA (Photo credit should read TONY KARUMBA/AFP/Getty Images)
Hoto: Tony Karumba/AFP/Getty Images

Sashen 'yan sanda ne yafi fama da cin hanci a Najeriya

Amma bayyana cewa ba'a samu wani canji ba a kan wannan batu ya haifar da ja-in-ja a tsakanin kungiyoyin da ke yaki da wannan bala'i da ya afkawa Najeriyar, kuma ya ke zama mai yi mata dabaibayi daga duk wani yunkurin ci-gaba.

Rahoton na Transparency International dai ya gano cewa har yanzu sai jama'a sun bada cin hanci  kafin su samu biyan bukatu a fannoni guda takwas da suka hada da neman lafiya a asibiti da samun  guraben karatun boko da ma aiyukan 'yan majlisu. Inda sashin 'yan sanda ya kasance wanda yafi fuskantar ta'azarar cin hanci da rashawa. Dr Kole Shatima na kungiyar Marc Arthur da ke Abuja wanda jigo ne a kungiyoyin da ke yaki da cin hanci da rashawa ya ce abin takaici ne abinda ya afkawa wadannan fannonin.

"Ai wadannan sassan da kungiyar Transparency International ta nuna sassa ne da a ko yaushe mutane ke neman a biya masu bukatunsu, a banagren gwamnati dai 'yan sanda sune mutane ke yawan mu'amalla da su domin samun biyan bukatarsu, kuma bangaren shari'a suma suna cikin wadanda ke hulda da jama'a. Wadannan su ne ya kamata suce a daina cin hanci da rahswa, to abu ne mai tada hankali domin su da ya kamata su hana amma su ne kan gaba a wannan matsala fiye da sauran sassan na aikin gwamnati."

Nigerian President Goodluck Jonathan speaks during a nationwide live broadcast on the state television on May 14, 2013. President Goodluck Jonathan has declared state of emergency in the nation's troubled northeast states of Yobe, Borno and Adamawa, where Islamic extremists now control some of the country's villages and towns, promising to send more troops to fight what is now an open rebellion. AFPPHOTO/PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Shugaba JonathanHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Matsayin gwamnatin Najeriya a kan matsalar cin hanci a kasar

To sai dai sakamakon rahoton bai yi wa jami'an gwamnatin Najeriyar dadi ba, wadanda suka dade da ikirarin cewa lallai ana samun ci gaba. Malam Ahmed Gulak shi ne mai baiwa shugaban Najeriyar shawara na musamman a fannin harkokin siyasa.

"Wannan rahoto ba lallai bane ya zama na gaskiya domin a wanan mulki na shugaba Goodluck Jonathan ba'a taba yaki da cin hanci da rashawa ba irin wannan. Kowa ya sani a kasar nan cewa mutanen da ake zarginsu da rub-da ciki a kan kayan jama'a an gabatar das u a gaban kotu. Don haka hukunta su ba hakki bane na shugaban kasa, ba hakki bane na ministoci, hakki ne na shari'a".

A wanan karon dai kungiyar ta Transparency International ta yi amfani da wani sabon salo wajen binciken nata, inda maimakon kwararru su gudanar da binciken, tambayoyi kai tsaye aka yiwa mutanen kasashen da aka gabatar da jerin sunayensu.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita       : Saleh Umar Saleh