Karshen taron AU a birnin Abuja | Labarai | DW | 09.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karshen taron AU a birnin Abuja

Shugabannin kasashen Afrika sun kammala taron su a Abuja a game da shirin zaman lafiya a Dafur ba tare da cimma wani tudun dafawa ba. An shafe kusan shekaru biyu ana tattaunawar shirin zaman lafiyar a birnin na Abuja tsakanin gwamnatin Sudan da bangarori biyu na yan tawayen kasar ba tare da wani cigaba ba, yayin da a waje guda shawarwarin ke tafiyar hawainiya. Shugaban kasar Congo Dennis Sassou Nguesso kuma shugaban kungiyar gamaiyar Afrika tare da shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo sun yi kokarin kai taron ga cimma wata matsaya amma hakan bai samu ba. Sun gana da mataimakin shugaban kasar Sudan Ali Osman Taha da shugabannin yan tawayen da kuma jakadu dake shiga tsakani domin sasantawa. Yunkurin zaman lafiyar dai na da nufin kawo karshen yakin basasa na tsawon shekaru uku a yankin Dafur wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 180,000. Shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo ya shaidawa manema labarai cewa za su sake wani taron domin dinke barakar dake tsakanin bangarorin. Shugaban tawagar Sudan a shawarwarin Majzoub al-Khalifa yace an sami yan nasarori musamman a kan batutuwa da suka shafi rabon arzikin kasa, da mukaman gwamnati da kuma shaánin tsaro.