SiyasaAfirka
Janye dakarun kiyaye zaman lafiya daga Sudan
December 23, 2020Talla
Da gagarumin rinjaye a daren wannan Talata da ta gabata aka kada kuri'ar na rashin tsawaita lokacin dakarun na kiyaye zaman lafiya sakamakaon matsin lamba daga gwamnatin wucin gadin Sudan da Rasha gami da wasu kasashen Afirka.
Tun shekara ta 2007 dakarun kiyaye zaman na Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Tarayyar Afirka suke aiki a lardin na Darfur da ke yamamcin Sudan. Akwai sojoji da 'yan sanda 6,000 gami da ma'aikata fararen huka fiye da 1,500.
Ita dai kasra ta Sudan tana kan hanyar komawa tafarkin dimukuradiyya tun bayan kawo karshen gwamnatin Shugaba Omar al-Bashir a watan Afrilun shekarar da ta gabata ta 2019. Rikicin na Darfur ya kai ga mutuwar kimanin mutane 300,000 yayin wasu milyan biyu suke tsere daga gidajensu.