1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takunkumin Turai kan man fetur din Rasha

February 3, 2023

Rasha ta bayyana cewa takunkumin da kasashen Turai suka kakaba wa man fetur da take fitarwa ta teku zai kara dagula hada-hadar makamashi a duniya.

https://p.dw.com/p/4N4Ok
Russland Rede Putin zur Schlacht von Stalingrad
Hoto: AP Photo/picture alliance

A lokacin da yake bayani a birnin Moscow, Dmitri Peskov da ke zama kakakin fadar shugaban Rasha ya tabbatar da cewa kasarsa na daukar matakan kare tattalin arzikinta daga barazanar takunkumin.

A ranar lahadi mai zuwa ne wannan takunkumin zai fara aiki, kuma sakatariyar zartarwa ta Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta nuna cewa wannan takunkumi zai rage wa Rasha samun zunzurutun kudi da ya kai miliyon 160 na yuro a duk rana.

Sai dai masana kasuwacin man fetur sun ce takunkumin na Turai na iya haifar da hauhawar farashin man fetur a Turai. Amma wasu kasashe sun fara karkata ga Amirka da kuma Saudiyya don cike gibin da suke samu a fannin man fetur da sauran makamashi.