Karin takunkumi ga Koriya ta Arewa | Labarai | DW | 07.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karin takunkumi ga Koriya ta Arewa

Kasar Amirka ta sha alwashin sake kakabawa Koriya ta Arewa takunkumi bisa shirin Koriyan na nukiliya.

Mataimakin shugaban ksar Amirka Thomas Pence

Mataimakin shugaban ksar Amirka Thomas Pence

Mataimakin shugaban kasar Amirka Mike Pence ne ya yi wannan alwashin, inda ya ce za su kara tsaurara takunkumi ga Koriya ta Arewan. Pence ya nunar da hakan ne bayan da ya tattauna da Firaministan Japan Shinzo Abe a birnin Tokyo, yana mai cewa Amirka da kawayenta za su kara daukar matakan kakaba tsauraran takunkumai ga Koriya ta Arewan bisa ci gaba da take yi da shirinta na nukiliya, inda ya ce har matakan soja za su dauka idan bukatar hakan ta taso.