1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan karin harajin kayayyaki a Najeriya

Uwais Abubakar Idris
March 20, 2019

Majalisar datawan ta amince da sabon albashi na Naira dubu 30 ga maikatan abinda ya haifar da murna da farin ciki daga ma’aikatan, to sai dai gwamnatin ta ce sai ta kara harajin kayayyaki

https://p.dw.com/p/3FMNZ
Nigeria Geld Geldscheine Naira in Lagos
Hoto: Getty Images

Tuni ma'aikatan suka fara maida martani da ma duba tasirin matakin na gwamnati ga sauran al'ummar Najeriya da basa karbaar albashi.

Amincewa da sabon albashin na Naira dubu 30 da majalisar ta yi ya  kawo karshen tsuguni-tashin da aka dade ana yi a tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadagon Najeriyar da ta kaisu ga yajin aiki na gargadi a kan lamarin, bisa cewa albashi mafi kankanta da suke karba a yanzu na Naira 18 a kowane wata koda kofar gida baya kaisu, balle ai maganar wata guda.

Tuni dai kungiyoyin ma'aikata suka shiga murna a kan karin da aka yi musu cike da fata ta ganin an sanyawa kudurin hannu don ya zama doka, suna mishi kashedin karin ya haifar da sabbin wahlhalu.

Gwamnatin dai ta tattauna da majalisa a kan Karin albashi da ta ce dole sai ta kara farashin kayayyaki daga kashi biyar cikin dari zuwa kashi 6.75 ko kashi 7.25. Tana mai kashedin kara harajin kayayyaki a kasar.

A yayin da ma'ikatan gwamnatin Najeriya ke murnar babban kalubale na ga kananan kamfanonin da ke da ma'aikatan da suka zarta goma da bisa doka dole su biya sabon albashi a yanayin da suke kuka da yanayin da suke ciki.