1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karim Wade ya shiga hannun hukumomi

April 18, 2013

An jefa Karim Wade, ɗan tsohon shugaban ƙasar Senegal Abdoulaye Wade a gidan kaso bisa zarginsa da yin sama da faɗi da dukiyar ƙasa

https://p.dw.com/p/18Ilx
AUSSCHNITT AUS: Karim Wade, right, son of Senegalese President Abdoulaye Wade waits in line to cast his vote for president at a polling station in Point E, in Dakar, Senegal Sunday, Feb. 26, 2012. After weeks of riots, Senegalese voters began casting their ballots Sunday in an election that threatens the country's image as one of the oldest and most robust democracies in Africa. This normally unflappable nation on the continent's western coast has been rocked by back-to-back protests following the decision of its 85-year-old leader to seek a third term. (Foto:Tanya Bindra/AP/dapd)
Karim WadeHoto: AP

An jefa Ɗan tsohon shugaban ƙasar Senegal Abdoulaye Wade a gidan kaso bayan da kotu ta tuhume sa da lafin cin hanci da rashawa, inda ake zargin ya kwashi dukiyar da ya kai yawan miliyan dubu guda na euro.

Karim Wade wanda ya riƙe muƙaman gwamnati daban-daban lokacin da mahaifinsa ke mulki, ya tafi gidan kason ne cikin tsauraran matakan tsaro, kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana.

Wasu mutane bakwai da ake zargi da hannu wajen yin sama da faɗi da dukiyar ƙasar kuma na tsare a hannun hukumomin.

Ana zargin Karim Wade mai shekaru 44 na haihuwa, da mallakan manyan kamfanoni da gidaje a gida da waje ta hanyoyin da basu dace ba, waɗanda suka haɗa da kamfanin da ke kula da shige da ficcen kayyaki a babbar tashar Containan da ke babban birnin ƙasar wato Dakar da ma wani bankin Morocco mai suna BCME

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu