A nada lauyan nan dan Kasar Birtaniya Karim Khan a matsayin babban alkali mai shigar da kara na kotun kasa da kasa wato ICC ko CPI da ke a birnin Hague.
Karim Khan ya maye gurbin Fatou Bensouda 'yar kasar Gambiya wacce ta kwashe shekaru 12 a kan matsayin. Khan zai fara aiki ne da manyan ayyuka a gabansa na kaddamar da bincike a game da rikici tsakanin Isra'ila da Falasdinu da batun Afghanistan da kuma Philipins.