1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kagame na karbar bakuncin taron Commonwealth

June 20, 2022

kasar Ruwanda na karbar bakuncin taron kolin shugabannin kasashe rainon Ingila (CHOGM), wanda ke hada shugabanni da wakilai daga kasashe 54. Shugaban Ruwanda Paul Kagame na amfani da damar wajen daukaka kasarsa a duniya.

https://p.dw.com/p/4Cwpt
Feierlichkeiten zum Tag der Streitkräfte in Mosambik
Shugaba Kagame ya yi amfani da bikin ranar sojojin Mozambik wajen yada angizonsaHoto: Estácio Valoi/DW

Haɓaka rawar da mata ke takawa a harkokin shugabanci, da haɓaka kasuwanci a tsakanin ƙasashen Commonwealth, da tallafa wa matasa a harkar shugabanci, na daga cikin muhimman batutuwan da wakilan ƙasashen Commonwealth da shugabannin za su tafka muhawara a kai a birnin Kigali na ƙasar Ruwanda a tsawon kwanaki 6. Matasan da suka halarci taron sun fara taron ne da tattaunawa kan makomarsu da yadda shugabanni ke neman maida kujerar mulki tamkar na gado.

Wani matashi ya ce wannan "wata dama ce a gare mu, da za mu iya bayyana kanmu game da batutuwa daban-daban da suka shafi matasa, ta fuskar kasuwanci da aikin yi." Yayin da wani ya ci gaba da nuna muhimmanci da taron da yake da shi a gare su, ya ce yana ba su "damar haɗin kai da kuma yin amfani da damammaki daban-daban da ke tsakanin ƙasashe daban-daban, mambobin Commonwealth da kuma shugabannin matasa."

Ruanda Kigali | Commonwealth Gipfeltreffen CHOGM
Sakatariyar Commonwealth Patricia Scotland ta yi jawabi a taron mata a KigaliHoto: SIMON WOHLFAHRT/AFP

Akwai shugabannin matasa sama da 350 da masu fada a ji a wajen taron da ke yunƙurin kawo sauyi a fannin tafiyar da harkokinsu. Ministar matasa ta Ruwanda, Rosemary Mbabazi, ta ce lokaci ya yi da matasa za su nuna cewa a shirye suke, maimakon neman uzuri na rashin samun damar yin jagoranci.

Mary Mbabazi ta ce: "Kuna yin abin da ya dace don ƙirƙirar makomarku? Ko kun bar damar? Na yi imanin cewa wadannan mutane ne da suke halarta ba sa ba da uzuri. Ba ma son a samu shugabanni masu yawan uzuri. Don haka babu uzuri."

Masu suka da kungiyoyin kare hakki sun ce bai kamata kasar Ruwanda ta dauki nauyin gudanar da taron ba saboda kaurin suna da ta yi a fannin kare hakkin dan Adam. Sai dai Michela Wrong, wata marubuciya ta Birtaniya kuma tsohuwar ‘yar jarida ta bayyana ta ce Paul kagame: "Ya dade da mayar da babban birninsa ya zama allon talla na duniya. Kuma cin nasarar matakinsu ya kasance wani ɓangare na tallace-tallacensa na duniya."

Ruanda Kigali | vor Commonwealth Gipfeltreffen
Ruwanda ta sanya tutar Kwango duk da rikicin da ke tsakaninsuHoto: Luke Dray/Getty Images

Wani batu da ya mamaye taron mutane kusan 5,000 ciki har da Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu wanda Yerima Chrles zai wakilce ta , shi ne zargin Ruwanda da goyon bayan 'yan tawayen M23 da ke yaki da dakarun gwamnati a DR-Kwango. Bugu da kari, rikicin baya-bayan nan tsakanin 'yan sandan Rwanda da masu zanga-zangar Kwango ya haifar da damuwa kan tsaro ga wakilan.