Karfafa rundunar Minusma a Mali | Labarai | DW | 26.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karfafa rundunar Minusma a Mali

Shugaba Issoufou Mouhamdou na Jamhuriyar Nijar ya ce dole a kara karfin aikin rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali ta yadda za ta iya yin yaki kungiyoyin 'yan ta'adda.

Shugaba Isssoufou na kalaman ne a yayin wata hira da manema labarai, inda ya kara jadadda bukatar cewa ya zama wajibi Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU, ya zama wajibi da ta samu wakilici a kokarin kasashen duniya na samun mafita kan rikcin kasar Libiya da yaki ya daidaita.

Issoufou Mouhamadou da ke magana da yawun takwarorinsa na kasashen Sahel da na yammacin Afirka, ya kara da cewa, "rikicin Libiya ya haddasa mumunar illa ga kasashen sahel da wasu kasashen Afirka, saboda hakan ba za ta yiwu ba a kaurace kasashen na Afirka wajen magance shi", tare da nuna bukatar kafa manzo na musamman na Majalisar Dinkin Dunyia da AU a Afirka da zai wakilci bangarorin biyu.