Karfafa huldar DW da gidajen radiyo a Najeriya | Zamantakewa | DW | 01.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

 

Karfafa huldar DW da gidajen radiyo a Najeriya

Tashar DW da kafofin yada labarai a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya za su ci gaba da hada kai domin karfafa aikin yada labarai don cimma nasarorin aikin musamman ganin an fara samun zaman lafiya  

Nigeria Interview mit Flüchtlingen in Maiduguri (DW/Al-Amin Mohammed)

Thomas Mösch na DW da Yalchilla Bukar ta Dandal Kura a Maiduguri suke hira da wadanda rikicin Boko Haram ya shafa

Ziyarar da Shugaban sashin Hausa na rediyon DW Thomas Mösch ya kai yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, ita ce irin ta ta farko tun da aka fara samun zaman lafiya a shiyyar, wacce ta shafe sama da shekaru shida ana fama da rashin tsaro.

Da isar sa a Maiduguri hedkwatar jihar Borno, Malam Mösch ya gana da shugabannin kafafen yada labarai na gwamnatin jihar Borno inda aka zaga da shi ya ga irin kayayyakin aikin da kafafen yada labarai mallakar jihar ke da su.

Daga bisani shugaban sashin Hausa na rediyon DW, ya gana da manema labarai inda ya shaida musu makasudin ziyarar sa. A gidan radiyon kasa da kasa na Dandal Kura, kuwa shugaban na Malam Mösch ya yi tattauanawa ta mintuna 25 a shirin bakon mu na mako. 

Nigeria Ibrahim Biu mit Thomas Mösch (DW/Al-Amin Mohammed)

Shugaban gidan rediyon Progress Ibrahim Biu da Shugaban sashen Hausa na DW Thomas Mösch a Gombe

Malam Mösch ya ce kafofin yada labarai na shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya za su amfana da dangantakar da suke yi da tashar DW, kazalika ita ma DW za ta amfana daga wannan alaka. A bangarensa shi ma Alhaji Faruk Dalhatu shugaban gidan rediyon Dandal Kura, ya bayyanan cewa dangantakar DW da kafafen yada labarai a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, za ta baiwa dukkan bangarorin riba, domin shi ya dade yanan hulda da tashar DW.

Daga jihar Borno Malam Mösch ya je jihar Bauchi, inda bayan ya gana da shugabannin kafar yada labarai mallakar jihar Bauchi, kana ya kuma mika kyauta ga wanda ya lashe gasar kachichi-kachichi na wasan Bundesliga da sashen Hausa na DW ya shirya.

Shugaban sashin Hausa na rediyon DW, ya karkare ziyarar ta sa ne a gidan radiyo Progress da ke Gombe, inda aka yi shiri da shi na tsawon awa guda tare da baiwa masu saurare dama bufa waya domin yi masa tambayoyi kai tsaye, a yayin ziyararsa ta Bauchi da Gombe.

A Gombe Malam Mösch, ya gana da manema labarai, inda daga bisani shugaban gidan rediyo Progress, wanda kuma tsohon ma'aikacin gidan rediyon DW Alh Ibrahim Biuya, bayyana jin dadi da ziyarar wacce ita ce irin ta farko a gidan rediyoyin.

A dukkanin jihohin da Shugaban sashin Hausa na rediyon DW Thomas Mösch ya ziyar ta, mutane sun yi mamakin yadda yake yin Hausa, musamman a Gombe da ya bayyana cewa yana cin tuwo miyar kuka.