1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karfafa hulda tsakanin Burkina Faso da Cote d'Ivoir

Salissou Boukari
July 18, 2017

Kashashen Burkina Faso da Cote d'Ivoir da dukannin su suka fuskanci hare-haren 'yan ta'adda, sun amince da hada karfi waje daya domin yakar duk wasu ayyukan ta'addanci a tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/2gkgm
Alassane Ouattara und Roch Marc Christian Kabore
Shugaban kasar Cote d'Ivoir Alassane Ouattara, da takwaransa na Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré.Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Shugaba Roch Marc Christian Kaboré na Burkina Faso da takwaransa Alassane Ouattara na Cote d'Ivoir ne suka sanar da wannan mataki a wannan talatan a birnin Ouagadougou na Burkina Faso yayin wani babban zaman taro na shekara-shekara karo na shida kan karfafa huldar dangantaka da ta kasuwanci tsakanin kasahen.

Shugabannin biyu sun ce ya na da babban mahimmanci kuma cikin gaggawa kasashen biyu su dukufa kan wannan batu na yaki da ta'addanci a tsakanin kasashen. Kasashen biyu kuma sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi akalla guda 20 cikin su har da batun samar da wutar lantarki daga Cote d'Ivoir zuwa Burkina Faso, da kuma kara tsawaita layin dogo da ya hada kasashen biyu.

Kasashen na Cote d'Ivoir da Burkina Faso dai na da kyaukyawar hulda tun da dadewa, wanda kafin zuwan Turawan mulkin mallaka suke a matsayin kasa daya. Yanzu haka dai a kalla 'yan Burkina Faso miliyan uku ne ke zaune a kasar Cote d'Ivoire.