Karfafa dangantakar China da Japan | Labarai | DW | 26.10.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karfafa dangantakar China da Japan

Sakamakon takun sakar da ke tsakanin China da Amirka dangane da batun kasuwanci, China na kokari na sake habaka dangantakar tattalin arziki da ke tsakaninta da makwabciyarta Japan.

Peking Abe bei Xi

Firaministan Japan Shinzo Abe da shugaban kasar China Xi Jinping

Tuni ma dai Firaministan kasar Japan din Shinzo Abe da taakawaransa na Chinan Li Keqiang suka gana a Bejing babban birnin kasar ta China. Yayin tattaunwar tasu, Abe ya  bayyana ganawar da wani muhimmin abu mai dinbin tarihi da ya afku tsakanin kasashen biyu. Haka kuma kasashen biyu za su hada hannu kan batutuwan da suka shafi kiwon lafiya da harkokin kudi da ma batun Koriya ta Arewa. A karshen ziyarar tasa a China karo na farko cikin shekaru bakwai, Firaminista Abe ya gana da shugaban kasar Chinan Xi Jinping.