1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karar Odinga game da magudin zabe

Halimatu AbbasMarch 16, 2013

'Yan sanda a Kenya sun yi amfani da hayaƙi mai sanya hawaye dan tarwatsa magoya bayan Fraiminista Raila Odinga wanda ya shigar da kara gaban kotun ƙolin ƙasar

https://p.dw.com/p/17z3U
Hoto: Getty Images/AFP

Fraiminista Raila Odinga ya shigar da kara gaban kotun ƙolin ƙasar ne dan neman ta soke zaben shugaban kasar da aka gudanar inda ya ke zargin cewa ko ɗaya ba'a kamanta adalci ba.

Wannan ƙara na Odinga na zuwa ne mako guda bayan da Uhuru Kenyatta, ɗan Jomo Kenyatta wanda ke ɗaya daga cikin waɗanda suka girka ƙasar ta Kenya ya lashe zaɓen da fiye da kashi 50 na ƙuri'un. Shi dai Odinga na neman kasar Kenya ta sake gudanar da zaɓe. Lauyansa ɗan asalin Amirka ne wanda ya taɓa wakiltan tsohon shugaban Amirka George W, Bush, kamar yadda mai magana da yawun jam'iyyar tasa, Eliud Owalo ya bayyana.

Daga cikin korafe-ƙorafen da ya yi har da rashin ingancin naurorin tantance sunayen masu zaɓe kasancewar daga farkon zaɓen kimanin katuna dubu 330 naurar ta nuna cewa lalatattu ne, amma bayan da aka fara amfani da hannu sai kuskuren ya yi sauƙi.

Magoya bayan Odinga dai sun ce sun yi imani da kotun ƙolin ƙasar kuma sun ce duk hukuncin da ta yanke, zai nuna ra'ayin talaka.

Mawallfiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Halima Balaraba Abbas