Karancin kudin shiga ga Afirka sakamakon faduwar farashin danyun kaya | Siyasa | DW | 09.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Karancin kudin shiga ga Afirka sakamakon faduwar farashin danyun kaya

Faduwar farashin danyen mai, karancin kudi ga kasa, kudaden shiga da kasashen Afirka ke samu sun ragu. Duk da haka nahiyar na ganin tana da damarmaki ga masu zuba jari.

Symbolbild Ausfall der Ölpreise

Najeriya ta fi kowace kasar Afirka Kudu da Sahara arzikin mai, ta shiga tsaka mai wuya saboda faduwar farashin

Duk da faduwar darajar kudi, matsalar cin hanci da karbar rashawa da ya jefa al'umma cikin hali mawuyaci na rayuwa, da kuma koma baya da ake samu a bangaren albarkatun kasa, har yanzu Afirka nahiya ce da ke da damarmaki masu dumbin yawa a fannin kasuwanci, har ma ga masu zuba jari na Tarayyar Jamus. An nunar da haka a taron inganta dangantakar kasuwanci tsakanin kasashen Afirka da Jamus a birnin Berlin.

Taron na wannan karon dai ya samu halartar manyan 'yan kasuwa da wakilan gwamnatoci daga nahiyar ta Afirka, da ke zama wurin da kowa ke hangen yana bunkasa kuma zai zame wani dandali ne na hada-hadar kasuwanci nan gaba. Shugaba John Dramani Mahama na kasar Ghana yana halartan taron na Berlin da nufin jan hankalin 'yan kasuwar Jamus zuwa zuba jari a kasashen Afirka.

"A matsayinka na mai zuba jari, me kake nema? Abun da kake nema shi ne wurin da ya dace domin gudanar da kasuwancinka, kuma ina ganin Ghana za ta bada wannan damar: kama daga demokradiyya da 'yanci da adalci zuwa albarkatu na kasa masu inganci. Kuma wadannan su ne shika-shikan tattali da ke bunkasa".

Koma bayan karfin tattalin arziki

A shekaru takwas da suka gabata ne dai aka gano daya daga cikin filayen mai mafi girma a nahiyar Afirka a Ghana. Zuba jarin da ake bukata domin hakar man kasar ya taimaka wajen inganta tattalin arzikinta da wajen sama da kashi 10 cikin 100. To sai dai a baya bayannan an samu koma baya inda a yanzu haka Ghana ke sa ran bunkasar tattali na kashi biyar kacal cikin 100, wanda Jamus sai dai ta yi mafarkinsa.

Ghana Präsident John Dramani Mahama

Shugaban Ghana John Dramani Mahama a taron huldar kasuwanci tsakanin Jamus da Afirka

Sai dai yanzu Ghana ba ta cikin kasashen Afirka masu karfin tattalin arziki, sakamakon faduwar farashin albarkatun kasa a kasuwannin duniya. A yanzu haka ganga guda na mai ba ya shige dalar Amurka 50. A shekaru biyu da suka gaba farashin ya ninka haka sau biyu.

A cewar Matthias Wacher na hukumar kula da kamfanonin tarayyar Jamus ta BDI dai, wannan yanayi ya jagoranci koma baya a fannin zuba jari.

"Faduwar farashin albarkatun kasa yana shafar tattalin arzikin kasashen Afirka masu yawa. Yanayin da ya jefa kasafin kudi cikin wani hali, da karancin kudi wajen gudanar da ayyukan raya al'umma. 'Yan kasuwa na Jamus suna da wannan masaniyar".

Shekaru biyar ke nan da Ghana ta hade a kungiyar kasashen da ke fitar da mai zuwa ketare. Amma cikin wannan dan lokaci lamuran gaba daya ya dogara kan kudaden da take samu daga cinikin mai.

Gibin kasafin kudi na karuwa

A shekara ta 2014 dai, kusan dalar Amurka miliyan 940 suka shiga aljihun gwamnati. Kama daga wannan lokacin ne gwamnati ke kasafin da ke sa ran samun kudi makamancin hakan zai dore.

Ölboom in Ghana

Masunta a garin Takoradi mai arzikin man fetir a Ghana

Faduwan farashin mai a kasuwannin duniya, ya jefa kasar ta Ghana cikin wani wadi na tsaka mai wuya. Kuma tuni aka fara ganin haka a cikin kasar, da a yanzu darajar kudinta wato Cedi ke faduwa, a yayin da basussukanta ya karu da wajen kashi 67 cikin 100. Tuni dai bankin duniya ya yi gargadin cewar, dogaron da kasar ke yi a kan fitar da albarkatu, zai haifar da cikas a gareta.

Chiara-Felicitas Otto, jami'a ce a kamfanin bayar da shawarwari kan harkokin kudi na Exficon da ke Ghana:

"Yanzu Ghana tana fuskantar mawuyacin hali. Yanzu da farashin mai ya fadi, kudaden da ya kamata su shiga asusu kamar yadda aka tsara, za su gaza".

Kwararrun 'yan kasuwa sun hakikance cewar, akwai wasu damarmaki masu yawa da nahiyar Afirka ke da su, maimakon dogaro a kan albarkatun mai da na kasa da mafiya yawan kasashen nahiyar ke da su. Kuma shiga daga cikin 10 na kasashen da tattalinsu ke bunkasa a duniya, na Afirka ne wadanda kuma ba sa dogaro da albarkatun karkashin kasa.

Sauti da bidiyo akan labarin