Karancin fitar mutane a zaben gwamnoni a Najeriya | Siyasa | DW | 11.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Karancin fitar mutane a zaben gwamnoni a Najeriya

Rahotanni daga sassa daban-daban na Najeriya na cewar an samu karancin fitar mutane wajen kada kuri'unsu a zaben gwamnoni da na 'yan majalisa da ake gudanarwa.

Labarin da muka samu daga jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya na cewar jama'a da dama ba su fita kada kuri'a a zabukan na yau ba musamman ma a cikin garin Kaduna din da kuma Zariya wanda ke zaman birni na biyu mafi girma a jihar, to amma a hannu guda wakilimu a Kaduna din Ibrahima Yakubu ya ce babu wani labari da aka samu na tashin hankali.

Can ma a yankin arewa maso gabashin Najeriya musammam ma jihar Gombe da Yobe da Borno zaben na gudana lami lafiya sai da a nan din ma ba a fita ba sosai. Wakilinmu Al-Amin Sulaiman Muhammad ya ce ba a fuskanci matsala da na'urar na ta tanatnce masu kada kuri'a ba kuma mata da dama sun samu fita don kada kuri'arsu.

A Kano ma dai an samu kamfa ta fitar masu kada kuri'a kamar yadda wakilinmu Nasir Salisu Zango ya shaida mana sai dai komai na tafiya ba tare fuskantar wata matsala ba. haka ma dai abin ya ke a jihohin Sokoto da Kebbi da Zamfara da Katsina.

A yankin Niger Delta kuwa labarin ya sha bamban da na sauran sassan jihar domin an samu tashin hankali a wasu yankunan jihar har ma an rasa mutum guda kamar yadda wakilinmu da Fatakwal a jihar Rivers Muhammad Bello ya shaida mana. Baya ga tashin hankali, rahotanni daga yankin na cewar an samu fuskanci sace-sace na akwatunan zabe sai dai jami'an tsaro sun ce sun sake matsa kaimi wajen ganin an kammala zaben lafiya.