Karancin abinci ga masu cutar Ebola a Liberiya | Siyasa | DW | 15.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Karancin abinci ga masu cutar Ebola a Liberiya

Shirin abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ya himmatu wajen ganin ba a fuskanci karancin abinci ba a wuraren da cutar nan ta Ebola ta yi kamari a kasar Liberiya.

Wannan shawarar da Majalisar Dinkin Duniya ta yanke dai ta biyo bayan fargabar da aka fara samu ta fuskantar karancin abinci a wasu yankuna da aka hana shige da fice sakamakon bullar Ebola a kasar ta Liberiya, lamarin da ake ganin zai iya kaiwa ga dagula lamura.

Wani abu har wa yau da ya sake sanyawa aka matsa kaimi domin kaiwa ga yanke wannan hukunci shi ne matakin da kamfanonin jiragen ruwa da na sama suka dauka na dakatar zirga-zirga da kai kayan abinci da sauran kayayyaki zuwa kasar ta Liberiya tun bayan da cutar ta bulla a kasar.

Südsudan UNAMIS Soldaten 22.12.2013

Majalisar Dinkin Duniya ta yi alkawarin sada mabukata da isasshen abinci

Da ta ke tsokaci danagne da wannan shirin na tallafawa Liberiya da abinci, mai magana da yawun shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya Fabienne Pompey ta ce za su yi amfani ne da jiragen sama domin yin jigilar kayan abinci kuma za a rika shiga da su zuwa kasar ta Liberiya ce daga Conakry dake kasar Gini domin sada shi ga mabukata.

Wannan tallafi dai inji Ms. Pompey zai fi karkata ne ga iyalan wanda wannan cuta ta hallaka da wadanda aka killace su don kula da lafiyarsu walau don sun kamu da cutar ko kuma don irin alamun da suka nuna na kamuwa da ita.

Zentralafrikanische Republik Bangui Alltagsleben

Kimanin mutane miliyan guda ne ke fuskantar barazanar yunwa a Liberiya

Kazalika tallafin zai isa ga mafarautan da aka haramtawa gudanar da sana'arsu tun bayan da cutar ta bulla a kasar kasancewar hukumomin lafiya sun bayyana cewar kwayar cutar ta samo asalinta ne daga namun daji musamman ma dai birrai da jemagu da makamantansu.

Liberiya dai na daga cikin kasashe na yammacin Afirka da wannan cuta ta fi yi wa ta'adi, wannan ne ma ya sanya hukumomin kasar suka sanya dokar ta baci a wani mataki na dakile kara bazuwar cutar wadda kan yi kisa cikin gaggawa.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin