1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hasashe kan abinci a Najeriya

Mohammad Nasiru Awal
November 1, 2019

A wannan makon sharhin labarun jaridun na Jamus a kan nahiyar Afirka wasu jaridun sun yi gargadi bisa raguwar abinci a Najeriya bisa illolin tsaro da kuma rufe kan iyakokokin kasar.

https://p.dw.com/p/3SLvI
Nigeria Maisfeld Bewässerung
Hoto: DW

A sharhinta jaridar Die Tageszeitung wadda ta leka Tarayyar Najeriya tana mai cewa yawan kayan abinci da Najeriyar ke samarwa ya ragu yayin da bukatar abincin ta karu. Jaridar ta ce yaduwar rikice-rikice na masu daukar makami da matsalar garkuwa da mutane, musamman a yankin arewacin kasar, hadi da matakin gwamnati na takaitawa ko ma haramta shigo da kayayyaki daga ketare ta hanyar rufe kan iyakokin kasar, yana tasiri kai tsaye a kan aikin samar da kayan abinci a kasar mafi yawan al’umma a Afirka. Jaridar ta ba da misali da alkalumman Hukumar Abinci da Aikin Gona ta Majalisar Dinkin Duniya da ke cewa, a bana hatsi da Najeriya za ta girba zai kasa da kashi 3 cikin 100 idan aka kwatanta da na bara. Shinkafa za ta ragu da kashi 10 cikin 100. A daidai lokacin da yawan al’ummarta ke karuwa da kashi 2.5 cikin 100 a kowace shekara. Sakamakonsa farashi na hauhawa saboda karancin abinci a kasuwa.
 
Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta leka kasar Mozambik, tana mai cewa a lokacin da aka gudanar da zabe a kasar makonni biyu da suka wuce, masu sa ido sun leka arewacin kasar, inda 'yan tarzoma da ke kiran kansu „Sojojin Khalifa“ suka addabi lardin Cabo Delgado da ke kan iyaka da kasar Tanzaniya. Sau da yawa dai ba a samun labarai daga yankin saboda matakin da gwamnati ta dauka na hana ‘yan jarida shiga yanki, sannan ta bar sojojin Rasha na yi wa 'yan yawon bude ido rakiya. Jaridar ta ce ba abin mamaki ba ne da gwamnatin ta Mozambik ta koma neman taimako daga tsohuwar abokiyar dasawarta don kawo karshen rikicin. Domin a shekarun bayan nan Rasha na karfafa hulda ta tattalin arziki da kasar. Kuma ba a dade ba da aka sanya hannu kan wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin Mozambik karkashin jagorancin jam’iyyar Frelimo da kamfanin hakan mai na Rasha wato Rosneft, yarjejeniyar da ta ba wa 'yan Rasha izinin aikin hako rijiyar iskar gas a Mozambik. Kimanin shekaru takwas da suka wuce aka gano arzikin gas a lardin na Cabo Delgado.
 
Cututtuka irin su maleriya wato zazzabin cizon sauro na yaduwa, wannan shi ne taken labarin da jaridar Neue Zürcher Zeitung ta buga bayan hira da ta yi da wakiliyar Asusun Taimakon Yara na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Sudan ta Kudu, Sandbu Ryeng wadda ta yi tsokaci dangane da ambaliyar ruwa da ta addabi Sudan ta Kudu. Ko da yake ambaliyar ruwa ba sabon abu ba ne a kasar, amma yawan ruwan sama fiye da kima da aka samu babu kakkautawa tun daga watan Yuli zuwa watan Oktoba, abu ne mai tayar da hankali. Kasancewa kasar na fama da karancin wuraren ba-haya, a dole mutane na ba-haya a fili, abin da kuma ke garwaya da ruwa yana kuma kwarara cikin koguna da ake samun ruwan sha a ciki. Da haka cututtuka irin su maleriya da amai da gudawa ke yaduwa tsakanin al’umma musamman kananan yara. A halin da ake ciki mutane da yawa na fama da sarar maciji. A sabili da ambaliyar su ma macizan na gudu daga ruwa zuwa kan tudu, inda suke cin karo da dan Adam.

Zika Moskito
Hoto: picture-alliance/dpa/O. Rivera
Mosambik Gaza Provinz  Mouzinho Gondorujo
Hoto: DW/C. Matsinhe