Kara samun shan kwayoyi tsakanin matasa | Zamantakewa | DW | 26.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Kara samun shan kwayoyi tsakanin matasa

Hukumomi da kungiyoyin da ke yaki da shan miyagun kwayoyi a Najeriya sun koka dangane da karuwar kwankwadar kwayoyi tsakanin matasa da matan aure

Hukumomi da kungiyoyin da ke yaki gadan-gadan a kan hana shan muggan kwayoyi da fataucin su a Nigeria kokawa suke yi dangane da karuwar matasa da ke lalacewa da matsalar tabun hankali saboda shaye-shayen abubuwan da ke rikirkita masu kwakwalwa na zamani da kuma hade-haden wasu sinadiran da ke chaza masu kai.

Mr Jona Ayuba Bakut shi ne dai shugaban kungiyr Drugs Abuse and Rehabilitation Centre a Nigeria inda ya nuna bacin ransa ga matsalar da suka janyo karuwar matasa mashaya a cikin al'umma da suke taimakawa wajen tayar da zaune tsaye a cikin kasa.Mallam Lawal Muduru wanda aka fi sani da suna Malam Nigger da ke kulawa da kimanin matasa sama da 1,600 masu fama da tabun hankali saboda shaye-shaye cewa ya yi akwai bukatar dakile safarar kwayoyin da matasa ke amfani da su.

Mr Oyinshi Daniel Ogbonna shi ne dai makaddashin shugaban tsare-tsare na hukumar da ke yaki da fataucin miyagun kwayoyi a Nigeria da ke bayyana matakan da suke dauka na dakile barbazuwar kwayoyi a cikin al'umma. Ya tabbatar da cewa an cafke daya daga cikin manyan masu safarar kwayoyin.

Medikamente in Nigeria

Tuni da sarakunan gargajiya da malaman addinai da kungiyoyin matasan unguwanni suka fara kaddamar da hari tare da gargadi ga masu sayar wa da shagunguna na chemist da shago-shago, wajen daina sayar da maganin tari ga matasa, da wasu matan aure, matukar dai in ba da takardan umurni ni ba daga wurin likita, domin rage sayar da maganin tari ga mashaya.

Sauti da bidiyo akan labarin