1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karin kudaden haraji ga kayayakin kamfanonin Amirka a China

Abdoulaye Mamane Amadou
August 23, 2019

Shugaban Donald Trump ya bayyana cewa Amirka za ta mayar da martni da kakkausar murya game da matakin da kasar China ta dauka na kara kudin fito ga kayan kamfanonin Amirka a China.

https://p.dw.com/p/3OPBa
Symbolfoto Fahnen USA und China
Hoto: picture-alliance/R. Goldmann

Tuni dai shugaban ya bukaci kamfanonin Amirka da su dauki wasu kwararan matakai kan kayan da suke samarwa a China, inda Donald Trump ya ce Amirkar ba ta bukatar China domin tana iya tafiya da ita ko ba ita.

A baya dai kasar China ta bayyana anniyarta ta kara kudade kimanin dala biliyan 75 na kudin fito ga daukacin kayayakin da ke shiga kasar da su daga kasar Amirka, matakin da kuma ya kara haifar da zaman doya da manja da aka jima ana fuskanta tsakanin kasashen biyu.