Kara karfin Iraki kan yaki da ′yan IS | Labarai | DW | 04.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kara karfin Iraki kan yaki da 'yan IS

Ostareliya za ta kara taimaka wa Iraki ta fanin tsaro domin kawar da masu neman kafa daular Islama a kasar Iraki.

Firaministan kasar Ostareliya Tony Abbott ya isa Bagadaza babban birnin kasar Iraki, domin duba hanyoyin karkafa dakarun kasar domin tinkarar mayaka masu neman kafa daular Islama. Abbott tare da takwaransa Haider al-Abadi, sun tattauna kan hadin kai a fannin aikin soji, da suka hada ba bai wa dakarun Iraki horo.

A wani labarin mataimakin shugaban kasar ta Iraki Nuri al-Maliki wanda ya kasance tsohon firaministan kasar, ya yi kakkausar suka bisa yadda 'yan siyasa suka rarraba kan al'ummar kasar tsakanin mabiya Sunni da Shi'a. Al-Maliki ya ce 'yan kasar suna rayuwa tare da juna, amma 'yan siyasa suna kawo rarrabuwa, kuma shi kansa an zarge lokacin da yake rike da madafun iko da janyo rikicin da ya sake ritsawa da kasar bayan janyewar dakarun Amirka.