1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kano: An amince da kara yawan masarautu

Ahmed Salisu
May 8, 2019

Gwamnatin jihar Kano ta amince da kara yawan masarautun jihar bayan da majalisar dokokin Kano din ta yi gyara ga dokar masarautun gargajiya ta jihar.

https://p.dw.com/p/3IBi3
Nigeria Wahlkampf von APC-Partei in Kano
Hoto: Salihi Tanko Yakasai

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu kan gyaran da 'yan majalisar dokokin suka yi wa dokar masarautun gargajiya a jihar Kano bayan da majalisar ta amince kan kara yawan masarautun jihar inda a yanzu yawansu ya kai biyar.

Baya ga masarautar Kanon da ake da ita, an amince da samar da sabbin sarakuna masu daraja ta daya da suka hada da Sarkin Gaya da Sarkin Rano da Sarkin Bichi Da kuma Sarkin Karaye. Majalisar dai ta shiga zaman sirri ne a wannan Larabar (08.05.19) kafin daga bisani ta dawo ta kuma tabbatar da wannan gyara da ta yi wa dokar.

Da ya ke tabbatar da dokar a zaman majalisar, shugaban majalisar dokokin jihar Kano din Hon. Kabiru Alhassan Rurum ya bayyana cewar mafi rinjayen 'yan majalisar sun gamsu da tabbatar da wannan doka.