1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Kanku Musa: Shugaban ma'adanai

Philipp Sandner MAB/MNA
December 17, 2020

Sarkin daular Mali Kanku Musa ya kasance mutum mafi karfin arziki da aka taba samu a duniya. Wadatarsa ta ba shi damar maida Timbuktu cikin birni mai ban mamaki. Ya yi sarauta tsakanin shekarar 1313 zuwa 1337.

https://p.dw.com/p/3mp1p
African Roots | Kanku Musa

Mene ne abu na farko da ya kamata a sani a kan Kanku Musa?

An haifi Kanku Musa a shekara ta 1280 a garin Manden. Ko da yake ana yawan kiran shi Kankan Musa, amma ainihin sunansa "Kanku". Wannan sunan mata ne da ya samo asali daga dangin mahaifiyarsa: Wasu daga cikin manyan kabilun wancan lokacin sun fi danganta yaro da bangaren uwa, don haka maza ma suke daukar sunan mahaifiyarsu. A cikin shekarar 1313, bayan rasuwar wansa Sarki Abu Bakr II, Musa ya zama shugaban Daular Mali. A lokacin mulkinsa na tsawon shekaru da dama, ya yada al'adun Musulunci a kewayen kasar Mali, kuma daular ta zama daya daga cikin wadanda suka ci gaba a duniya.

Me ya sa Kanku Musa ya shahara a duniya?

Kanku Musa ya fito ne daga gidan sarauta na su Keita wadanda suka yi mulkin Mali tsawon karnoni da yawa. Ya kasance sarki mai wadata wanda ya gina daula mai karfin gada a ji, kuma wacce ta bunkasa. Bisa ga bayanan al'adar baka, kakansa Abu Bakr na farko, kani ne ga Sunjata Keita wanda ya kafa Daular Mali. Sarautar Musa ta haska daular Mali a duniya.

Mene ne burin Kanku Musa na daular Mali?

Wanda ake kiransa Mansa ("Sarki") Musa, "Mai Nasara na Ghanata" ko "Ubangijin ma'adinan Wangara", Kanku Musa yayi mulki a lokacin da aka samu wadatar albarkatun karkashin kasa. Ana daukarsa a matsayin daya daga cikin mutanen da suka fi arziki da aka taba samu a rayuwa. An kiyasta cewa arzikinsa ya kai biliyan 400 na Dalar Amirka a cewar wasu majiyoyin. A lokacin mulkin Kanku Musa, ya bunkasa kasuwancin nesa. Zinare da gishiri sune asalin tushen masarautar.

Kanku Musa: Shugaban ma'adanai

Ta ya ya Kanku Musa ya nuna dukiyar daular sa?

A shekarar 1324, Kanku Musa ya tafi aikin hajji a Makka. Ayarinsa ya kunshi mutum dubu 60 da bayi dubu 12 da dogarai da ke sanye da kayan kawa da sanduna na zinare wadanda kuma ke kula da dawakai da kayansu. Wannan kasaitaccen rangadin ya sa ya zama sananne, musamman a Yammacin Afirka da yankin Gabas ta Tsakiya. A cikin kowane gari da ya ya da zango, Musa ya kasance mai karamci sosai kuma ya yi ta ba da kyautar wani bangare da dukiyarsa - wanda babu shakka yayi tasiri ga tattalin arzikin yankin, da kuma labarin mulkinsa.

Me mutane ke tunawa game da kamun ludayin Kanku Musa a daular?

Sakamakon dimbin arzikin da ya mallaka, Kanku Musa ya gina wuraren addini da na mulki da yawa daga shekarar 1325. Daga cikinsu akwai masallatai, da makaranta da kuma masarauta a garuruwan Timbuktu da Gao. Masallacin Sankoré da ke Timbuktu ya kasance fasaharsa da ta fi fice. Ya ba da damar musayar al'adu tsakanin kasar Mali da kasashen Larabawa. Wasu daliban Mali sun je  Misra da Maroko don kammala karatunsu, yayin da wasu malaman Masar da Moroko suka je karatu a Sankoré madrasa. A wancan lokacin ya kasance cibiyar yada kyakkyawan al'adun Musulinci a Yammacin Afirka.

Shawarwarin kimiyya kann wannan makalar ya samu ne daga masanin tarihi Farfesa Doulaye Konaté, da Dakta Lily Mafela, Ph.D., da kuma Farfesa Christopher Ogbogbo. Gidauniyar Gerda Henkel ce ta daukar nauyi shirin Tushen Afirka.