Kanada: Trudeau ya yi tazarce karo na biyu | Labarai | DW | 22.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kanada: Trudeau ya yi tazarce karo na biyu

Jam'iyyar Justin Trudeau ta Liberal ta sake darewa kan karagar mulki a kasar Kanada a karo na biyu, a wani zabe da aka yi wanda ta sha da kyar.

Da kyar da gumin goshi, firaiministan Kanada Justin Trudeau ya sake lashe zabe karo na biyu, amma duk da haka wakilan jami'iyyarsa ta masu sassaucin ra'ayi sun rasa rinjaye a majalisar dokoki.

A yanzu wajibi ne Trudeau ya gudanar da mulkin kasar Kanada tare da hadin gwiwar jam'iyyar adawa ta Demokrats da wasu tsirarun jam'iyyun da ke kasar, abinda ke zama kalubale ga mulkinsa da ma jam'iyyarsa a wa'adi na biyu na samun amincewa da dokoki.