1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango: Shekara guda da mulkin Tshisekedi

January 24, 2020

Shekara guda kenan da Shugaba Felix Tshisekedi ya kama ragamar mulkin jamhuriyyar Dimokradiyyar Kwango sai dai batun ja-in-ja da ya ke da bangaren adawa ya mamaye jaridun kasar.

https://p.dw.com/p/3Wlnw
Demokratische Republik Kongo | Félix Tshisekedi | Provinzparlament Upper Katanga
Shugaba Felix TshisekediHoto: Presidence RDC/G. Kusema

Yayin da Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ke cika shekara guda kan madafun iko, har yanzu wasu na ganin ja-in-ja tsakanisa da 'yan adawa ce ta dauki hankalinsa cikin watanni sha biyun da ya jagoranci kasar. Wannan dai shi ne ke sanya masu nazarin al'amura a ciki da wajen kasar ke ganin ci gaba dai a Kwangon zai yi wahalar samuwa, muddin shugaban ya ci gaba kan tsarin da ya ginu a kansa.


Ana iya cewa hankalin masu nazarin harkokin siyasa a ciki da wajen Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na kan Shugaba Felix Tshisekedi ne, wanda zai cika shekara guda kan mulki a gobe Asabar, 25 ga watan Janairu, a matsayin shi na shugaban kasa.Koda yake an kawar da yiwuwar biki na musamman saboda bikin shekarar guda kan mulki, mutane da dama musamman masharhanta za su yi amfani da kafafen watsa labarai wajen bayyana yadda kamun ludayin shugaban ya kasance tsawon lokacin, inda wasu za su kushe wasu kuma su yaba, bisa al'ada.

DR Kongo Felix Tshisekedi beim Kinshasa Digital Forum
Shekara guda da Shugaba Felix Tshisekedi ya kama ragamar mulkiHoto: Präsidentschaft der DR Kongo/G. Kusema

Ana dai zargin wasu matakan boye da tsohon shugaban kasar, Joseph Kabila wanda ya taimaka wajen kai Tshisekedin ga mulki, na taka rawa wajen hana shugaban cika alkawurarn da ya yi wa 'yan kasar ta Kwango. Wasu daga cikin manazarta lamura yanzu a kasar na cewa dole ne sabon shugaban ya sake lale muddin da'awar tasa ta kawo ci gaba a Kwango za ta cimma gaci. 

 

Duk da hakan dai ana iya cewa Shugaba Felix Tshisekedi, ya yi kokarin yin wasu abubuwan da za su iya dadada wa wasu 'yan kasar a siyasance, masalan kokari da yake yi na shafe suna da tagomashin tsohon Shugaba Kabila da ya mulki kasar shekaru 18, ta hanyar daga danginsa shi ma kasancewar mahaifinsa Etienne Tshisekedi, shi ne madudugun adawar kasar lokacin da yake raye.

 

Amma har yanzu masu kallon lamuran irin su Dieudonné Mushagalusa, na cewa dole ne shugaban ya yi la'akari da abin da ya yi mai alfanu ga rayuwar 'yan kasar. Duk dai da kyautuwar dangantakar Kwangon da kasashen duniya, 'yan kasar da ke kallon lamura za su ci gaba ne da sa ido kan tafiyar gwamnatin na Shugaba Tshisekedi tare ma da yi mata fida a kullum, saboda kaurin suna da suka yi wajen sukar shugabanni ko da kuwa a ina suka sami kansu a duniya.