1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Salla Karama bayan Azumin Ramadana

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 5, 2022

A Litinin biyu ga watan Mayun da muke ciki ne, aka gudanar da bukukuwan Sallah Karama a mafi yawa daga cikin kasashen duniya. Sallar ta bana ta gudana ne bayan kammala azumin watan Ramadana da a bana aka yi guda 30.

https://p.dw.com/p/4At6d
Karamar Salla I Najeriya I Lagos
ukukuwan Salla Karama ta banaHoto: Adeyinka Yusuf/AA/picture alliance

Al'ummar Musulmi a fadin duniya, sun gudanar da shagulgulan Salla Karama cikin annashuwa. Koda yake a kasashe da dama kamar Najeriya, bikin Salla Karamar ya riski al'umma cikin halin kuncin rayuwa sakamkon matsin tattalin arziki, sai dai hakan bai hana al'ummar Musulmin irin wadannan kasashe nuna farin cikinsu sakamakon riskar watan na Shawwal da kuma kammala Azumin Ramadana lafiya ba.

Duk da cewa a mafi akasarin kasashen duniya ciki kiuwa har da Tarayyar Najeriya an gudanar da Karamar Sallar a ranar Litinin biyu ga watan Mayun da muke ciki bayan cika Azumin Ramadana 30, a wasu kasashe kamar Jamhuriyar Nijar da ke makwabtaka da Tarayyar Najeriyar an yi Salla Karama a ranar Lahadi bayan azumi 29.