Kamfanin motocin Daimler ya aikata zamba | Labarai | DW | 13.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kamfanin motocin Daimler ya aikata zamba

An dai yi zargin cewa kamfanin ya siyar da motoci sama da miliyan daya a Turai da Amirka wadanda injinsu aka yi masa kwaskwarimar da ba zai bada bayanan hakikanin iskar da ke gurbata muhalli da suke fitarwa ba.

Wani bincike da kafafan yada labarai na Jamus suka fitar a ranar Laraba ya gano cewa kamfanin nan mai hada motoci na Daimler, wanda ke hada motocin Mercedes-Benz tsawon kusan shekaru goma ya ailkata zamba cikin aminci inda na'urar tantance gurbatacciyar iska da motocin kamfanin ke fitarwa basa bada sahihan bayanai. An dai yi zargin cewa kamfanin ya siyar da motoci sama da miliyan daya a Turai da Amirka wadanda injinsu aka yi masa kwaskwarimar da ba zai bada bayanan hakikanin iskar da ke gurbata muhalli da suke fitarwa ba.

Mahukunta a Jamus sun gudanar da bincike a inda ake hada motoncin na Daimler tun daga watan Mayu kamar yadda binciken hadin gwiwar kafafan yada labaran na WDR da NDR da jaridar Süddeutsche ya nunar. Binciken ya ce injinan motocin na OM 642 da OM 651 na amfani da wata na'ura da aka haramta amfani da ita wacce ke boye hakikanin gurbatacciyar iskar da motocin ke fitarwa. Mai magana da yawun kamfanin na Daimler dai yaki cewa komai game da binciken sai dai  sai dai ya ce kamfanin na ci gaba da yin biyayya ga binciken da mahukunta ke yi.