1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kame shuagabannin FDLR a Jamus

November 18, 2009

Mahukuntan Jamus sun cafke shuagabannin ƙungiyar FDLR da ake zargi da laifukan kashe-kashe na gilla da fyaɗe da cin mutuncin ɗan-Adam a Kwango

https://p.dw.com/p/KaFk
Yara na fama da raɗaɗin yaƙin KongoHoto: AP

Ɓangarorin da ke da hannu a rikicin Rwanda na ci gaba da samun banbancin ra´ayi dangane da kama shugabannin ƙungiyar 'yan tawayen Hutu ta FDLR da aka yi jiya a nan Tarayyar Jamus.

Cikin wata sanarwar dake ɗauke da sa hanun babban magatakardarta, ƙungiyar ta FDLR ta bukaci gwamnatin Jamus da ta hanzarta sakin shugabannin 'yan tawayen Hutu biyu da ta cafke saboda a cewar uwar ƙungiyar, ba su da hannu a cikin kisan ƙare dangin da ake zarginsu da aikatawa a gabashin Jamhuriyar Demoƙaraɗiyar Kwango da kuma Rwanda. Ta na mai cewa kashin kaji ne gwamnatin Kigali ke shafa wa shugabannin na FDLR . A saboda haka ne ma suka danganta Jamus da mai zama 'yar kazagin Ruwanda da Kwango.

Deutschland Ignace Murwanashyaka FDLR
Shugaban ƙungiyar FDLR Ignace MurwanashyakaHoto: AP

Shi dai Ignace Murwanashyaka mai shekaru 46,da kuma ke shugabantar ƙungiyar ta FDLR tun shakara ta 2001, an kama shi ne a birnin Karlsruhe na kudu maso yammacin Jamus inda yake rayuwa tun bayan da ya fara gudun hijira, yayin da shi kuma mataimakin nasa, Straton Musoni, mai shekrau 48 da haihuwa, 'yan sanda suka cafke shi a birnin Stuttgart, bisa izinin da kotun ƙoli ta kasar Jamus ta bayar tun ranar 16 ga watan nowamba.

Ulrus Delus da ke shugabantar sashinAafirka na ƙungiyar ƙasar Jamus da ke yanƙi da cin zarafin tsiraru a duniya ya nuna cewar ko shakka babu sun aikata wanna ta´asar.

Ya ce da akwai ƙwaƙƙwarar shaida da ƙungoyoyin Jamus masu zaman kansu da ma Majalisar Ɗinkin Ɗuniya ke dasu dake tabbatar da cewa sun aikata wannan ta´asar. Misali ana nandi muryoyinsu lokacin da suke buga waya ga dakarun a ana daf da kai farmaki da ya haddasa mace macen mutane da dama.

Kindersoldaten im Kongo
'Yan tawayen na amfani da yara ƙanana a aikin sojaHoto: GTZ

Jamhuriyar Demoƙaraɗiyar Kwango ta yaba da abin da ta kira namijin aiki da Jamus ta gudanar na mutunta yarjejniyoyin ƙasa da ƙasa da suka tanadi kame duk waɗanda a ke zargi da aikata kisan kiyashi , tare da hukuntasu, ko kuma miƙa su ga ƙasar da suka yi aika-aikan a cikinta. Kakakin gwamnatin na Kwango, Lambert Mende ya bukaci hukumomin ƙasashen Faransa da Amirka da su bi sahun Jamus wajen kame 'yan tawayen da ke ɓoye a cikin waɗannan ƙasashe domin a gurfanar da su a gaban kuliya.

Ita kuwa gwamnatin Rwanda cewa tayi kamata ma yayi a tasa ƙeyar waɗannan shugabannin 'yan tawayen FDLR zuwa Kigali domin fiskantar shari´a. Dama dai ita ƙasar ta Ruwanda ce ta bukaci gudunmawar sauran takwarorinta na duniya, na kame 'yan tawayen sakamakon zarginsu da taka rawa wajen gudanar da kisan ƙare dangi na Ruwanda a shekara ta 2004, da kuma kisan mummuƙe na gabashin Jamhuriyar Demoƙaraɗiyar Kwango.

Tarsis Karagarama, shi ne ministan shari'a na Ruwanda

ya kuma ce a garemu wannan yunƙuri na Jamus ya kawo ƙarshen zullumi da ake yi a Kwango da Ruwanda.Ya kuma ƙara da cewar:

"Muna fata dai sauran ƙasashen duniya za su bi sau domin ta haka ne za a tabbatar da cewar an ƙwanco ma kowa haƙƙinsa, kuma an yi ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a wannan yanki"

Kame Murwanashyaka da kuma Musoni da Jamus ta yi, ya zo a daidai lokacin da Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Ƙungiyar Gamayyar Turai ke ta neman hanyoyin ƙwance ma dakarun 'yan tawayen Ruwanda ta FDLR ɗamara. Ana zargin ƙungiyar da ta ƙunshi ƙabilar Hutu da aikata ta´asa a kan farar hula a shekarun 2008 da kuma 2009 a Kwango kama daga fyaɗe kan ɗaruruwan mata, har ya zuwa ƙona ƙauyuka da dama, tare da tilasa wa yara Kanana shiga aikin soja.

Edita: Mouhamadou Awal Balarabe

Edita: Ahmad Tijani Lawal