Kame masu safarar mutane a Italiya | Labarai | DW | 04.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kame masu safarar mutane a Italiya

Jami'an 'yan sanda a Italiya sun tarwatsa wani gungun masu safarar mutane a teku zuwa Turai tare da kame 23daga cikinsu, a gabar tekun Sicily da Rome da kuma wasu sassa a kasar.

Jami'an 'yan sanda a Italiya na ci gaba da sintiri a gabar teku

Jami'an 'yan sanda a Italiya na ci gaba da sintiri a gabar teku

'Yan sandan na Italiya sun sanar da cewa sun kuma kwace dubban kudi na euro a hannunsu. Wadanda ake zargi da yin safarar mutanen dai ana zargin sun fito ne daga wani gungu na fitattun tsageru da ke yin safafar mutane daga yankin Arewacin Afirka zuwa Arewacin nahiyar Turai ta barauniyar hanya, inda kuma suke biyowa ta cikin kasar Italiyan. An dai cafke mutanen ne bayan da wani tsohon mai safarar mutanen ya tona asiri inda har ma ya bayyana cewa ana kashe wasu mutanen domin a sayar da bangarorin jikinsu. Gungun masu safafar dai su 38 ake nema ruwa a jallo inda aka yi nasarar kama wasu 23 daga cikinsu, sai dai rahotanni sun nunar da cewa yanzu haka ana neman sauran da suka tsere wadanda suka hadar da 12 'yan asalin Eritrea da kuma wasu uku 'yan kasar Habasha wato Ethiopia.