Kame-kamen ′yan adawa a Masar | Labarai | DW | 28.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kame-kamen 'yan adawa a Masar

Hukumomin tsaro a Masar sun kama mutane fiye da dari kafin wata zanga-zangar da magoya bayan tsohon shugaban kasar Mohamed Morsi suka kira a wannan Jumma'a.

Ofisfin ministan tsaron cikin gidan kasar ta Masar ne ya sanar da kame mutane akalla 107, kafin zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati da suka shirya gudanarwa a wannan Jumma'a. Tun dai kifar da gwamnatin Mohamed Morsi, sabbin hukumomin kasar ta Masar ke shan gwagwarmaya tare da neman toshe duk wata kafa ta zanga-zanga ga magoya bayan tsofon shugaban kasar, inda ake zargin su da shirya zanga-zanga mai muni gami da tashe-tashen hankula.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Awal