1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici gabanin babban zabe a Kamaru

Ramatu Garba Baba
October 1, 2018

Rikici ya barke a wasu sassan kasar Kamaru, yayin da 'yan awaren yankin Ambazoniya na masu amfani da Turancin Inglishi ke gudanar da bikin cikar shekara guda da ayyana 'yancin kan yankin.

https://p.dw.com/p/35pPM
USA Untrerstützer von Kameruns Präsident Biya vor seinem Hotel in New York
Hoto: picture alliance/AP Photo/B. Matthews

Wannan lamari dai na zuwa ne kasa da mako guda a gudanar da zaben shugaban kasar ta Kamaru, lamarin da ya saka gwamnatin kasar kafa dokar hana fita da zirga-zirga da duk wasu tarukan jama'a a yawancin biranen yankin masu magana da harshen Turancin Ingilishin na Anglophone. Yunkurin da ya kasance mataki na neman hana wa 'yan awaren tayar da tarzoma.

Kamerun Sprachenstreit um Englisch
An sami barkewar rikici a wasu sassan KamaruHoto: Getty Images/AFP

Yanzu haka dai al'umar yankin na masu magana da harshen Turancin Ingilishin a kasar ta Kamaru na cikin zaman fargaba ta la'akari da asarar rayukan da aka samu a shekarar bara, lokacin dauki ba dadin da ya biyo bayan ayyana 'yancin kan yankin na Ambazoniya, inda 'yan sanda suka bindige masu zanga-zanga akalla arba'in. Wannan kasa da ke yankin tsakiyar Afirka mai mutane kimanin miliyan 25, ba ta taba fuskantar zabe a yanayi na tabarbarewar tsaro da ya yi muni kamar wannan karon ba, dalilin da ya sanya aka jibge jami'an tsaro a yankuna uku daga cikin goma na kasar.