1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Za a rufe wasu tashoshin zabe a yankin Anglophone

August 28, 2018

Hukumar zaben kasar Kamaru ELECAM ta sanar da cewa, dubban rumfunan zabe a yankunan da ke amfani da harshen Ingilishi za a rufe don barazanar da ke fitowa daga masu rajin ballewa daga kasar.

https://p.dw.com/p/33tT1
Kamerun Präsident Paul Biya
Hoto: imago/Xinhua Afrika

A saboda da matsalli na tsaro da kuma yadda ake fama da tashe-tashen hankula a yankunan da ke amfani da harshen Turancin Ingilishi na kasar Kamaru, hukumar gudanar da zaben kasar wato ELECAM ta sanar da cewa, dubban rumfuna zabe ne za su kasance a rufe a lokacin gudanar da zaben kasar na watan Oktoba. Mutane da yawa masu jefa kuri'a sun ce ba su amince cewa da za a tabbatar da tsaro ba.

Enow Abrams Egbe shi ne shugaban hukumar zaben ta ELECAM, wanda ya ce sun saurari korafin masu jefa kuri'a wadanda ke ta gunagunin cewa suna tsoron abin da zai faru da rayukansu idan suka fita don kada kuri'a a ranar 7 ga Oktoba mai zuwa a zaben shugaban kasa.

"Tabbas akwai matsaloli, ba kawai a arewa maso yamma ba, amma har da kudu maso yamma, mutane na tsoro. Za mu rage rumfunan zabe zuwa kalilan wanda hakan zai taimaka wajen tabbatar da kariya ga masu jefa kuri'a, da ma'aikatan hukumar zaben tare da kayan aikin."

Enow Abrams Egbe ya ce akalla tashoshin rumfunan zabe dubu biyu za a rufe a cikin yankunan da ake amfanin da Turancin Ingilishi kuma za a tura sojoji don kare masu jefa kuri'a.

Masu zanga-zangar neman hadin kan 'yan Kamaru
Masu zanga-zangar neman hadin kan 'yan KamaruHoto: picture alliance/AP Photo/B. Matthews

Wani mazaunin garin Bamenda mai suna Omer Yusimbom, ya ce duk da tabbatar musu da komai zai tafi daidai da aka yi, shi hankalinshi bai kwanta da hakan ba kuma ya ce ba zai fita zaben ba.

"Tuni sakonnin gargadi na bidiyo da na sauti ke yawo ana jan kunnen mutane cewa duk wanda ya fita ranar zabe duk abin da ya same shi to shi ya janyo wa kanshi. Saboda haka idan muka dubi irin wannan yanayi, ba za mu iya fita ba domin muna tsoron abin da ka iya faruwa da rayukanmu, babu tabbacin za a iya kare mu. Muna tsoron kasancewa tsakiyar masu tayar da kayar baya da sojoji."

Joseph Foyung mazaunin garin Buea ne wanda ya ce gwamnati ta bude tattaunawa ta gaskiya kuma ta dakatar da yakin da ta ke ikirarin ta fara da 'yan bindiga.

"Ban yi tsammani zan iya fita zabe a ranar 7 ga Oktoba ba. Na tuna a lokacin zaben 'yan majalisar dattijai, an yi garkuwa da sace wasu 'yan takara da ma masu jefa kuri'ar wanda sai da taimakon wasu shugabannin gargajiya aka samu suka sake su. Ba na tunanin zan fita zaben."

Fiye da miliyan guda cikin masu jefa kuri'a miliyan bakwai ne ke yankunan da ke amfani da harshen Ingilishi. Ana kuma tsoron ba za su iya jefa kuri'arsu ba ga daya daga cikin 'yan takara tara da ke fafatawa a yayin da ake gwagwarmayar fada tsakanin sojoji da 'yan bindiga a kowace rana. Akalla mutane 300 da suka hada da sojoji 130 sun mutu a rikicin.