Kamaru ta kori manyan hafsoshin soji biyu | Siyasa | DW | 04.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kamaru ta kori manyan hafsoshin soji biyu

Gwamnatin ta kori hafsoshin ne bayan sun sace kayan da aka tanada domin yakar kungiyar Boko Haram, da tallafawa masu gudun hijira

Jami'an gwamnatin kamarun sun yi zargin cewa an sace kudade da kayan abincin da al'ummar kasar ta bayar da gudunmawa domin taimakawa sojojin da kuma 'yan gudun hijira.

Da ya ke karin haske kan korar manyan jami'an sojojin biyu na Kamaru da Shugaba Paul Biya ya yi , Bokam ya ce an sallame su ne bisa samunsu da laifin sayar da kayan abincin da aka tanadarwa sojojin kasar da ke yaki da Boko Haram.

"Shugaban kasa ya yanke shawarar hukunta tsofaffin kwamandojin sojojin rundunar ne kuma dole sabuwar rundunar su martaba sabon alhakin da aka dora musu. Dole ne su sani cewa duk wanda bai kare kimar aikin da aka sanya shi ba, za a hukunta shi ba tare da bata lokaci ba."

Kamerun Armee Soldat Anti Boko Haram 11/2014

Sojojin Kamaru ba su shiga gefen iyakar Najeriya

Matakan kariya nan gaba

Babban kwamandan rundunar mayakan sama ta sansanin Yaounde kanal Martin Owona na daya daga cikin sojojin da aka kora daga aikin bisa zarginsa da hada baki domin sayar da abincin sojojin da aka ajiye a sansanin, inda ya yi karyar cewa ya lalace ne. Shin ko wani mataki wanda ya gajeshi kanal Alfred Mvondo zai dauka domin tabbabar da ganin an kaiwa sojojin abincinsu? Ga abin da ya ke cewa:

"Yanzu zamu dauki dukkan matakan da suka kamata domin neman tallafin kayan, da kuma tabbatar da cewa an damkasu ga hannun wadanda aka nemi taimakon dominsu. Zamu aike da kayan abincin zuwa sansanoninmu da ke garuruwan Garoua da Ngaoundere da kuma Bertoua. Za kuma mu fadawa mutanen da su tabbatar sun karbi kayansu, shi ne abin da muka kudirce."

Akwai kudin kula da jin dadin sojoji

A nasana bangaren minsitan kula da harkokin mulki na Kamarun da aka dorawa alhakin karbar karo-karon da akewa sojojin da kuma 'yan gududn hijirar, ya sanar da cewa a yanzu akwai kimanin dalar Amirka miliyan hudu a hannunsa domin kulawa da sojojin da ke yaki da Boko Haram din yana mai cewa:

Nordkamerun Grenze zu Nigeria Soldaten Anti Terror

Al'umma ce ta yi karo-karon kayayyakin tallafawa sojojin

"Abunda zai taimaka mana shi ne yin abubuwa a bayyane domin al'ummar Kamaru su sanar cewa kudaden taimakon da aka ba da zai kai ga wadanda aka taimakawa wato sojojin da kuma mutanen da suka tserewa bala'in Boko Haram. Mun lura cewa bukatar sanya kungiyoyin fararen hula da kuma wasu 'yan siyasa domin kula da kudaden, wata alama ce da ke nuni da yin abubuwan a bayyanae."

A watan Maris din da ya gabata ne dai gwamnatin Kamaru ta bukaci al'umma da su ba da tallafin kudade da kayan abinci da kuma na sawa domin taimakawa 'yan gudun hijirar da kuma sojojin da ke yaki da Boko Haram din, sai dai bayan da korafi ya yi yawa sai Shugaban Paul Biya na Kamaru ya bude asusun banki domin sanya kudaden da aka tara a ciki, ko da ya ke masu sanya idanu na cewa ba duka kudin da ya shiga asusun bane ya ke fita domin taimakon sojojin da 'yan gudun hijirar.

Sauti da bidiyo akan labarin