Kamaru ta fara tura sojinta kan iyakarta da Najeriya
May 27, 2014Talla
Wani babban jami'in tsaro ,ya ce an fara tura dakarun ne, a yau waɗanda suke isa zuwa kan iyakar gungu-gungu, wanda kuma ya ce sun shirya tura dakaru dubu ukku. Aikewa da dakarun da ƙasar ta Kamaru ta yi wacce ta raɓa iyaka mai tsawon gaske da Najeriya,na zuwa ne a ƙasa da makonnin biyu da kammala taron Faransa, wanda ya duba hanyoyi da za a bi don magance matsalar ta rashin tsaro a yanki.
Wacce ke zaman babbar barazana ga ƙasashen yankin waɗanda suka haɗa da Nijar da Kamaru da Chadi da kuma Benin. A wani labarin kuma a yau an ba da rahoton cewar 'yan Ƙungiyar ta Boko Baram; sun kashe jami'an tsaro 25 a garin Buni Yadi na Jihar Yobe.
Mawallafi : Abdourahamane Hasane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar