Kamaru ta ɗaukaka wasu sojojinta zuwa muƙamin Janar | Labarai | DW | 14.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kamaru ta ɗaukaka wasu sojojinta zuwa muƙamin Janar

Matakin ya shafi wasu manyan sojojin ƙasar da ke taka muhimmiyar rawa wajan yaƙi da Kungiyar Boko Haram a yankunan arewacin ƙasar masu Fama da hare-haren ƙungiyar.

A wannan Jumma'a Shugaban ƙasar Kamaru Paul Biya ya ɗaukaka wasu manyan sojan ƙasar da ke taka rawa cikin yaƙi da Ƙungiyar Boko Haram zuwa muƙamin birgediya Janar. Shugaban ya ɗauki wannan mataki ne a cikin wata sabuwar ayar doka wacce aka karanto a wannan Jumma'a a gidan radiyon gwamnatin ƙasar.

Matakin ƙarin girman dai ya shafi wasu manyan sojojin ƙasar ne su biyar da suka haɗa da Jacob Kodji da Bouba Dobekreo sojoji biyu da yau da shekara guda suke riƙe da daga a yankin arewacin Ƙasar mai fama da hare-haren Boko Haram. Sauran sojojin sun haɗa da Simon Ezo'o Mvondo shugaban runduna ta 11, da Valere Nka da Frederic Djonkep Kommandan sojojin yanki na ukku na ƙasar ta Kamaru wanda ya haɗe sauran yankuna biyu na arewacin ƙasar da ke a arewacin jihar Adamaoua ƙasar ta Kamru.

Sojoji dubu takwas da 500 ne dai ƙasar ta Kamaru ta girke a yankin arewa mai nisa na ƙasar domin yaƙar Ƙungiyar ta Boko Haram.