1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari kan 'yan sanda a Kamaru

Salissou Boukari
July 1, 2018

Wasu mutane dauke da makamai sun kai hari a ofishin 'yan sanda na garin Buéa da ke a matsayin babban birnin yankin da ake magana da Turancin Ingilishi a Kudu maso Yammacin kasar Kamaru.

https://p.dw.com/p/30dxf
Kamerun Sprachenstreit Englisch
Hoto: Getty Images/AFP

Shaidun gani da ido dai sun ce an ragargaza wani bangare na ofishin 'yan sandan da ke unguwar Munya, inda suka ce an ji karar harbe-harbe a cikin daran Asabar wayewar garin wannan Lahadin da harin ya afku. Wasu 'yan awaran kasar ta Kamaru sun ce wani gungun mayaka ne masu rajin ganin an raba kasar ta Kamaru suka kai wannan hari, sai dai gwamnatin ta Kamaru ba ta ce uffan ba kan lamarin.

Hare-hare gami da sace mutane,da ma kashe-kashe, ya zama ruwan dare gama duniya a yankin na Kamaru da ake magana da Turancin Ingilishi, inda sojojin kasar ke yakar mayaka 'yan aware. Kawo yanzu dai sojojin kasar ta Kamaru sama da 80 ne suka mutu sakamakon wannan rikici, sannan kuma an kashe daruruwan fararen hula.